Jigon Boko Haram da ke da hannu a sace ’yan matan Chibok ya shiga hannu
Wani jigo a kungiyar Boko Haram da ke da hannu a sace ’yan matan Chibok sama da 200 ya shiga hannu inji Hedkwatar Tsaro ta Sojan Najeriya. Rundunar Sojan ta ce jami’anta sun fasa wani gungun ’yan leken asiri na ’yan Boko Haram din ne tare da kama wani dan kasuwa da ta ce yana da […]
Wani jigo a kungiyar Boko Haram da ke da hannu a sace ’yan matan Chibok sama da 200 ya shiga hannu inji Hedkwatar Tsaro ta Sojan Najeriya.
Rundunar Sojan ta ce jami’anta sun fasa wani gungun ’yan leken asiri na ’yan Boko Haram din ne tare da kama wani dan kasuwa da ta ce yana da hannu dumu-dumu a sace ’yan matan.
Ma’aikatar tsaron ta ce dan kasuwar mai suna Babuji Ya’ari na da’awar shi dan banga ne da ke taimakawa wajen yakar Boko Haram, amma kuma dan ta’adda ne.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade ya ce Babuji Ya’ari ne ya jagoranci kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gwoza a watan Mayu; kuma shi ne ya tsara wasu hare-hare da suka hallaka daruruwan mutane a Maiduguri tun daga shekarar 2011.
Ya ce bayanin da suka samu bayan kama Ya’ari ne ya taimaka musu wajen kama wasu mata biyu da suka hada da Hajiya Kaka wadda ya ce ’yar leken asiri ce ga kungiyar da kuma ke sayo wa ’yan ta’addan makamai da kuma Hafsat Bako, wadda ita ce ke biyan maharan kungiyar ta Boko Haram bayan sun kai hari.
Wannan kamu ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a Jihar Borno da Abuja da Kaduna da Bauchi, inda jama’a da dama suka hallaka.