‘Jihar Bauchi za ta amfana da shugabancin Dogara’

Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi Alhaji Bala Abdullahi Mai’auduga ya bayyana farin ciki kan yadda ’yan majalisar wakilai suka zabi Barista Yakubu Dogara daga Jihar Bauchi a matsayin sabon shugaban majalisar. Alhaji Bala Mai’aduga ya ce Barista Yakubu Dogara wanda tsohon dan Jam’iyyar PDP ne da ya sauya sheka zuwa APC kuma […]

‘Jihar Bauchi za ta amfana da shugabancin Dogara’
‘Jihar Bauchi za ta amfana da shugabancin Dogara’

Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi Alhaji Bala Abdullahi Mai’auduga ya bayyana farin ciki kan yadda ’yan majalisar wakilai suka zabi Barista Yakubu Dogara daga Jihar Bauchi a matsayin sabon shugaban majalisar.

Alhaji Bala Mai’aduga ya ce Barista Yakubu Dogara wanda tsohon dan Jam’iyyar PDP ne da ya sauya sheka zuwa APC kuma mutanen mazabarsa ta Tafawa balewa/bogoro/Dass suka sake zabensa a karo na biyu, mutum ne mai kishin jama’arsa da tsayuwar daka wajen kare bukatunsu.
A cewarsa yankin Arewa maso Gabas da Jihar Bauchi za su amfana sosai da shugabancin Yakubu Dogara domin mutum ne mai gaskiya kuma yana kamanta adalci ga Musulmi da Kiristoci da ke mazabarsa.
Alhaji Bala Mai’auduga ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a shekaranjiya Laraba.
Ya ce tun lokacin da Barista Yakubu Dogara ya shiga harkokin siyasa yake bada gudunmawa wajen ci gaban Jihar Bauchi.