Jihar Bauchi za ta kashe Naira miliyan 120 don ciyar da masu azumi

Gwamnatin Jihar Bauchi za ta kashe Naira miliyan 120 domin ciyar da masu azumi a masallatai 124 a ciki da wajen garin Bauchi.Shugaban kwamitin ciyar da abincin azumi kuma Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Alhaji Salisu Ahmad Barau ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce za a kashe Naira miliyan 62 a […]

Jihar Bauchi za ta kashe Naira miliyan 120 don ciyar da masu azumi
Jihar Bauchi za ta kashe Naira miliyan 120 don ciyar da masu azumi

Gwamnatin Jihar Bauchi za ta kashe Naira miliyan 120 domin ciyar da masu azumi a masallatai 124 a ciki da wajen garin Bauchi.
Shugaban kwamitin ciyar da abincin azumi kuma Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Alhaji Salisu Ahmad Barau ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce za a kashe Naira miliyan 62 a cikin garin
Bauchi, yayin da za a kashe Naira miliyan 58 a yankunan kananan hukumomin jihar.
Ya ce tuni aka saki rabin kudin domin dafa abinci a masallatai ta hannun kwamitocin da aka kafa don aikin saboda ciyar da mutum 6,200 a kullum, kuma an yi tanadin ciyar da mutum 200 a kowane masallaci amma kuma ana samun kimanin mutum 500, don haka aka yi kiyasin ciyar da mutum dubu 10 a kullum a dukkan masallatan.
Alhaji Salisu Baarau ya ce mambobin kwamitin za su rika ziyartar masallatai domin duba yadda ciyarwar ke gudana, kuma kowane mutum daya daga cikin mambobin zai rika duba kananan hukumomi biyu domin a lura da yadda masallatan ke gudanar da aikin.  Ya ce idan kudi sun samu za a kara wa masallatan yawan masu shan ruwa.
Ya ce kwamitocin kananan hukumomi a bana za su gudanar da ciyarwar duk da cewa an samu jinkirin fitowar kudin, “amma yanzu aiki na gudana yadda ya kamata,” inji shi.
Ya bukaci jama’a su rika gudanar da addu’o’in fatar alheri ga kasa da shugabanni don a samu
ingantar al’amura. Kuma ya shawarci jama’a su rika taimaka wa ’yan uwansu a wannan wata domin samun falala da alherin da ke ciki.