Jihar Borno za ta dauki karin ma’aikatan lafiya

Za a dauki ungozoma da ma’aikatan jinya 20 don cike gibi a wasu asibitoci

Jihar Borno za ta dauki karin ma’aikatan lafiya

Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno.

Gwamnatin Jihar Borno za ta dauki ungozoma da ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya 20 don cike gibin da ake da shi a Asibitin Maryam Abacha da ke Maiduguri.

Haka kuma za a sanya na’urar samar da wutar lantarki daga hasken rana a Asibitin Mata Masu Hauhywa na Gwange domin inganta samar da tsaftataccen ruwan sha.

Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya amince da hakan ranar Alhamis lokacin da ya ziyarci asibitocin guda biyu.

Gwamnan ya kai ziyarar ne don gane wa idonsa yadda ake tafiyar da sauye-sauyen da ake yi wa bangaren kiwon lafiya a Jihar.

A Asibitin Maryam Abacha, ya kuma ba da umarnin gina ma likitoci da sauran ma’aikatan lafiya gidaje.

Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya da ta fito da sabbin dabaru don sayo karin magunguna da kayan aiki don taimaka wa mata masu juna biyu.