Jihar da yara miliyan biyu ba sa zuwa makaranta

Yara kimanin miliyan biyu ne ba sa zuwa makaranta a Jihar Zamfara, daga cikin yara fiye da miliyan 10 marasa halartar makaranta a Najeriya. Hakan ta sa gwamnatin jihar bullo da shirin sanya ilimin boko a tsarin makarantun allo da kuma ciyar da almajirai a makarantun. Manufar shirin ita ce, ”Ba wa wadannan yara damar […]

Jihar da yara miliyan biyu ba sa zuwa makaranta

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara

Yara kimanin miliyan biyu ne ba sa zuwa makaranta a Jihar Zamfara, daga cikin yara fiye da miliyan 10 marasa halartar makaranta a Najeriya.

Hakan ta sa gwamnatin jihar bullo da shirin sanya ilimin boko a tsarin makarantun allo da kuma ciyar da almajirai a makarantun.

Manufar shirin ita ce, ”Ba wa wadannan yara damar lakantar ilimin dukkanin bangarorin biyu, da kuma dakile matsalar barace-barace”, a cewar hukumar ilimin bai daya ta jihar.

Shugaban hukumar Abubakar Aliyu Maradun ya kara da cewa za a fara shirin ne yara 30,000 a makarantu 280 daga a kananan hukumomi takwas.

Ya ce ”An tanadi kayayyakin karatu, littattafan yara da kuma malaman, sannan muna ba su abinci sau daya a kullum”.

Jihar ta gano girmar matsalar yaran marasa zuwa makaranta ne bayan alkaluman da a baya suka nuna cewa yara miliyan daya ne a jihar ba sa zuwa makaranta.

Zamfara na daga jihohin da matsalar tsaro ta yi kamari, sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

Ayyukan bindiga a jihar sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama baya ga tilasta wa dubbai tserewa daga gidajensu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos