Jihar Filato ta bayar da hutun Laraba

Jihar Filato ta sanar da ranar Laraba a matsayin ranar hutun ma’aikatan jihar don samun damar kada kuri’arsu a zaben kananan hukumomin jihar da za ayi a gobe Laraba. Majiyarmu ta gano cewa, za a gudanar da zaben ne a kananan hukumomi 13 cikin 17 na jihar. An dai dage zaben kananan hukumomin Jos ta […]

Jihar Filato ta bayar da hutun Laraba

Jihar Filato ta sanar da ranar Laraba a matsayin ranar hutun ma’aikatan jihar don samun damar kada kuri’arsu a zaben kananan hukumomin jihar da za ayi a gobe Laraba.

Majiyarmu ta gano cewa, za a gudanar da zaben ne a kananan hukumomi 13 cikin 17 na jihar.

An dai dage zaben kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta kudu da Barikin Ladi da Riyom saboda kalubalen tsaro dake fuskantar yankunan.