Jihar Filato ta yi sabon Kwamishinan ’Yan Sanda

Kundunar ’Yan Sandan Najeriya ta turo Austin Agbonlahor a matsayin sabon Kwamishinanta a Jihar Filato. Agbonlahor zai maye gurbin Andie Undie a matsayin  Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Filato ne. Kakakin ’Yan sandan Jihar Filato, Tyopeb Terna ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya sa wa hannu a ranar Talatar da ta gabata. […]

Jihar Filato ta yi sabon Kwamishinan ’Yan Sanda

Kwamishinan ‘Yan Sanda, Austin Agbonlahor

Kundunar ’Yan Sandan Najeriya ta turo Austin Agbonlahor a matsayin sabon Kwamishinanta a Jihar Filato.

Agbonlahor zai maye gurbin Andie Undie a matsayin  Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Filato ne.

Kakakin ’Yan sandan Jihar Filato, Tyopeb Terna ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya sa wa hannu a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce, “An kawo sabon Kwamishinan ’Yan sanda, Austin Agbonlahor, kuma har ya kama aiki a Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato.”

Terna ya ce kafin a kawo Agbonlahor Jihar Filato, yana rike da matsayin Kwamishinan ’Yan sanda ne a Bangaren Gudanarwa a Hedikwatar ’Yan sanda da ke Abuja.

Kuma ya taba rike mukamin Kwamishinan ’Yan sandan  Jihar Neja.

Agbonlahor ya yi karatun digirinsa a Jami’ar Benin, ya kuma rike mukamai daban-daban a aikin ’yan sanda, ciki har da mukamin Daraktan Kwasa-Kwasai a Makarantar Koyon Aikin Dan sanda da ke Wudil a Jihar Kano.

Terna ya ce Agbonlahor ya yi aiki a dukan yankuna shida na Najeriya.