Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD
Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali.

Ƙungiyar Masu Nakasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe (JONAPWD), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Masu Nakasa ta Jihar, Dokta Isiyaku Adamu.
Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali.
- NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC
- Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah
Wannan taron na musamman, wanda aka gudanar a ofishin JONAPWD da ke Gombe, ya zama wata muhimmiyar dama don tattauna matsaloli, musayar ƙwarewa da kuma ƙarfafa fafutuka don kare haƙƙoƙin yara masu fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali.
A jawabinsa, Dokta Adamu ya bayyana cewa yara masu nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali na fuskantar manyan ƙalubale wajen samun ilimi mai inganci, kiwon lafiya mai nagarta da kuma shiga cikin al’umma.
Ya ce, wannan nakasa ta hankali da ta jiki tana nufin yanayi da ke shafar fahimtar ƙwaƙwalwa wajen koyo da hulɗa da jama’a.
Sai dai, Dokta Adamu ya yi nuni da cewa idan aka ba wa waɗannan yara goyon baya mai kyau da fahimta, za su iya bunƙasa basirarsu su yi fice, kuma su bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban al’umma.
Dokta Adamu ya kuma yi bayani ga iyaye game da dokar masu nakasa ta Jihar Gombe da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaba wa hannu kwanan nan. Ya bayyana dokar a matsayin wata gagarumar nasara da za ta tabbatar da kariya, ƙarfafawa da haɗa yara masu nakasa tare da iyalansu cikin al’umma.
Daga cikin muhimman kudurorin taron, akwai ƙarfafa yaƙin wayar da kai don isar da saƙon zuwa ga iyaye da masu kula da yara masu nakasa. Wannan zai taimaka wajen ƙarfafawa al’umma fahimtar baiwa da basirar da yara masu nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali ke da ita.
Hakazalika, Dokta Adamu ya nuna godiyarsa ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda jajircewarsa wajen inganta rayuwar masu nakasa ta hanyar zartar da dokokin da suka dace.
“Muna matuƙar godiya ga jagorancin gwamna da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da rayuwar masu nakasa ta inganta,” in ji shi.