Jihar Gombe za ta kashe sama da Naira biliyan 88 a bana

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ya mika wa Majalisar Dokokin Jihar, kasafin kudin bana na sama da Naira biliyan 88. Kasafin kudin mai taken ‘Kasafin Cika Buri,’ manufarsa shi ne kammala ayyukan da aka faro a jihar. Kasafin kudin ya hada da na ayyukan yau da kullum da suka kai Naira biliyan 46 […]

Jihar Gombe za ta kashe sama da Naira biliyan 88 a bana
Jihar Gombe za ta kashe sama da Naira biliyan 88 a bana

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ya mika wa Majalisar Dokokin Jihar, kasafin kudin bana na sama da Naira biliyan 88.

Kasafin kudin mai taken ‘Kasafin Cika Buri,’ manufarsa shi ne kammala ayyukan da aka faro a jihar. Kasafin kudin ya hada da na ayyukan yau da kullum da suka kai Naira biliyan 46 da miliyan shida da kuma na manyan ayyuka da suka kai Naira biliyan 42 da miliyan takwas. “Burin wannan gwamnati shi ne samar da ayyukan yi a tsakanin al’umma don magance fatara da kuma da ci gaban jihar,” inji Gwamnan. Gwamna dankwambo ya kuma ce za a samar da abubuwan more rayuwa da yaki da talauci da gina al’umma sannan a ciyar da yankunan karkara gaba. Gwamna dankwambo ya kara da cewa a cikin shekara uku na mulkinsa a kullum gwamnatinsa gina jama’a take yi ta wajen magance matsalolin da suka shafe su kuma ta bunkasa tattalin arzikin da ciyar da ilimi gaba. Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar ce ta samu kaso mafi tsoka na Naira biliyan tara da miliyan hudu sannan sai Ma’aikatar Gona, Naira biliyan biyu da miliyan takwas. Ma’aikatar Ilimi ta samu Naira biliyan biyar da miliyan daya, inda Naira biliyan biyu da miliyan hudu kuma za a kashe su ne a bangaren kiwon lafiya.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista