Jihar Kaduna ta kammala jigilar Alhazanta zuwa gida Najeriya 

Hukumar Jindadin Alhazan jihar Kaduna ta bayyana cewa, ta kammala kwaso Alhazanta daga kasa mai tsarki zuwa Najeriya. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar a yau Asabar a Kaduna. ‎A cewarsa, jirgin Fly Nas  wanda ke dauke da alhazan karshe […]

Jihar Kaduna ta kammala jigilar Alhazanta zuwa gida Najeriya 

Hukumar Jindadin Alhazan jihar Kaduna ta bayyana cewa, ta kammala kwaso Alhazanta daga kasa mai tsarki zuwa Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar a yau Asabar a Kaduna.

‎A cewarsa, jirgin Fly Nas  wanda ke dauke da alhazan karshe ya sauka a Kaduna ne da misalin karfe 1:01 a yau tare da Alhazai 390.

‎Darakta Janar ta Hukumar Kula da Addinai ta jihar Sheikh Jamilu Abubakar Albani da shugaba mai Kula da hukumar jin dadin Alhazan jihar Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara da kuma Sauran manyan jami’ai masu Kula da Alhazai duk suna cikin jirgin karshe.

Sanarwar ta kara da cewa, akalla Alhazai dubu  3,544 ne suka sauke farali a bana a yayin da mutum daya ya rasa ransa a Birnin Makka.

Sheikh Jamilu Abubakar Albani, ya mika godiyarsa ga Allah sannan ya yi godiya ga dukkan jami’an alhazan da sauran masu ruwa da tsaki da ma’aikatan hukumar a bisa gudunmuwa da suka bayar har aka samu nasara a aikin Hajjin bana.