Jihar Kaduna za ta fara rusau
Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA), ta gargadi jama’ar jihar su daina sayan filayen da aka kebe a Sabon Birnin Kaduna da ke Unguwar danbushiya inda ta sha alwashin rusa duk ginin da aka yi a yankin. Wannan gargadi na kunshe ne a takardar da aka raba wa manema labarai dauke da sanya hannun […]
Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA), ta gargadi jama’ar jihar su daina sayan filayen da aka kebe a Sabon Birnin Kaduna da ke Unguwar danbushiya inda ta sha alwashin rusa duk ginin da aka yi a yankin. Wannan gargadi na kunshe ne a takardar da aka raba wa manema labarai dauke da sanya hannun Kakakin Hukumar KASUPDA, Malam Nuhu Garba dan’ayamaka a madadin Shugabar Hukumar, Madam Saratu Musa Haruna. Ta ce yankin danbushiya da ke kusa da sabon birnin Kaduna, wuri ne da gwamnati ta kebe domin samar da birni mai tsari da kayan more rayuwa kamar ruwan sha da makarantu da sauransu. “Muna shawartar jama’a su guji gine-gine a yankin da sauran filayen da gwamnati ta kebe, muna kuma shaida wa masu gine-gine da aka sa musu alamar rushewa ko aka ba su takardar umarnin cirewa, to a bi umarnin kafin wa’adin da aka diba ya kare,” inji sanarwar. Hukumar KASUPDA ta yi gargadin cewa an dauki kwararan matakan kawar da duk gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a duk a fadin jihar. Hukumar ta yi kira ga jama’a su rika tuntubar hukumomi da suka dace kamar Ma’aikatar kasa da Safiyo da KASUPDA kafin kulla cinikin fili kuma a nemi iznin gini daga hukumar kafin farashi.