Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin duba matsalolin malaman firamare

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma Kwamishiman Ilimi na Jihar, Farfesa Hafiz Abubakar ya kaddamar da wani kakkarfan kwamiti na mutum shida don bincikowa tare da gabatar da matsalolin malaman makarantun firamare na jihar.Wata sanarwa da Kwamared Auwal Zakari Ayagi, Mai taimaka wa Shugaban kwadago na Musamman kan Kafofin Watsa Labarai ya aiko wa Aminiya ta […]

Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin duba matsalolin malaman firamare
Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin duba matsalolin malaman firamare

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma Kwamishiman Ilimi na Jihar, Farfesa Hafiz Abubakar ya kaddamar da wani kakkarfan kwamiti na mutum shida don bincikowa tare da gabatar da matsalolin malaman makarantun firamare na jihar.
Wata sanarwa da Kwamared Auwal Zakari Ayagi, Mai taimaka wa Shugaban kwadago na Musamman kan Kafofin Watsa Labarai ya aiko wa Aminiya ta ce an kaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis din makon jiya a ofishin Mataimakin Gwamnan.
Kafa kwamitin a cewar sanarwar ya biyo bayan korafin da kungiyar Kwadago reshen Jihar Kano a karkashin jagorancin Kwamared Kabiru Ado Minjibir (Magayakin Minjibir) ta gabatar wa Mataimakin Gwamnan ne a wata ziyara da ta kai masa, inda ta koka kan halin da malaman firamare suke ciki na rashin ciyar da su gaba na tsawon shekaru da rashin karin kudin albashi na shekara-shekara da sauransu.
Da yake kaddamar da kwamitin Mataimakin Gwamnan, wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar, Alhaji Umar Muhammad Jalo ya wakilta ya bukaci ’yan kwamitin su yi aikin cikin gaskiya da jajircewa don binciko matsalolin.
A jawabin shugaban kwamitin kuma Babban Kwamishina na 1 a Hukumar SUBEB, Alhaji Umar S. Muhammad ya yi alkawarin yin aiki tukuru don binciko maysalolin cikin lokacin da gwamnati ta diba musu.
An ba kwamitin mako uku ya mika rahotonsa ga gwamnati, kuma ayyukan da zai gudanar sun hada da binciko yawan malaman da suka cancanci a ciyar da su gaba amma ba a ciyar da su ba, da binciko wadanda aka ciyar da su gaban amma ba sa amfana da hakan.
Sauran sun hada da binciko dalilan da suka sa ba a yi wa malaman karamin kari na shekara-shekara da sauran matsalolin da suke da alaka da aikinsu.
Sauran wakilan kwamitin sun hada da Abdullahi Ibrahim Gwarzo daga Ma’aikatar Ilimi da Kimiyya da Fasaha da Kwamared Kabiru Ado Minjibir daga kungiyar Kwadago da wakili daga ofishin Shugaban Ma’aikata da Kwamared Muhammad A. Hambali daga kungiyar Malamai (NUT) da Balarabe Hassan karaye Daraktan mulki na Hukumar SUBEB a matsayin Sakataren Kwamitin.