Jihar Kano za ta rika ba kowane mabaraci Naira dubu 10 duk wata

Babban Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce gwamnatin jihar za ta rika ba kowane mabaraci tsoho da ba zai iya yin komai ba Naira dubu 10 a kowane wata a karkashin shirinta na hana bara a jihar.Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana haka ne matsayinsa na Babban Bako Mai […]

Jihar Kano za ta rika ba kowane mabaraci Naira dubu 10 duk wata
Jihar Kano za ta rika ba kowane mabaraci Naira dubu 10 duk wata

Babban Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce gwamnatin jihar za ta rika ba kowane mabaraci tsoho da ba zai iya yin komai ba Naira dubu 10 a kowane wata a karkashin shirinta na hana bara a jihar.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana haka ne matsayinsa na Babban Bako Mai jawabi, a wurin rufe gasar karatun Alkur’ani Mai girma na karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato da aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na Jos.
Ya ce a wannan shiri na hana bara a Jihar Kano,  almajirai wadanda ba za su iya koyon sana’a ba saboda tsufa, za a yi rajistarsu a dukkan kananan hukumonin jihar 44 inda za a rika ba kowannensu Naira
dubu 10 a kowanne wata domin su rika cin abinci.
Har ila yau ya ce an bude wa almajiran da za su iya koyon sana’a a dukkan kananan hukumomin jihar inda za a koya musu sana’o’i har 12.
Ya ce kananan yara kuma masu bara za a rika koyar da su a makarantun gwamnati kyauta. Ya ce a wannan tsari dukkan nakasassu za a rika ba su magunguna kyauta a asibitocin gwamnatin jihar.
Sheikh Aminu Daurawa ya ce hana bara ba karamin alheri ba ne a Arewa domin da barar ce ake zaginmu.
Ya ce gwamnatin jihar ta amince ta taimaka wa mata wadanda suke cikin wahala da jari, masu bukatar aure kuma a taimaka musu su yi aure, sannan masu bukatar komawa makaranta a taimaka musu su koma.
Ya ce muna da mata da kananan yara wadanda suke bukatar a taimaka musu, musamman a Arewacin kasar nan, don haka ya yi kira ga sauran jihohi kan su rungumi wannan shiri.
A gasar karatun Alkur’anin da ’yan takara 189 suka fafata Malam Muhammad Sani Ahmad ne ya zamo Gwarzon Shekara.