…Jihar Katsina ta biya Hukumar Hajji ta kasa Naira miliyan 757

Gwamnatin Jihar Katsina ta biya Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Naira miliyan 757 a matsayin cikaton kudin kujerun da aka ware wa jihar a aikin Hajjin bana.Babban Darakta a Hukumar, Alhaji Ahmad Hasan Dutsinma ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da jawabi wajen kaddamar da wayar da kan maniyyata aikin Hajjin a kananan […]

…Jihar Katsina ta biya Hukumar Hajji ta kasa Naira miliyan 757
…Jihar Katsina ta biya Hukumar Hajji ta kasa Naira miliyan 757

Gwamnatin Jihar Katsina ta biya Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Naira miliyan 757 a matsayin cikaton kudin kujerun da aka ware wa jihar a aikin Hajjin bana.
Babban Darakta a Hukumar, Alhaji Ahmad Hasan Dutsinma ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da jawabi wajen kaddamar da wayar da kan maniyyata aikin Hajjin a kananan hukumomin Dutsinma da Kankiya da Kurfi, inda ya ce gwamnatin ta biya kudin ne domin kada a rage wa jihar kujerun da aka ware mata.
Babban Daraktan ya yaba wa gwamnatin jihar bisa kokarin da take yi don ganin an samu nasarar aikin Hajjin bana. Sai dai ya nuna bacin ransa kan yadda wasu maniyyatan ba su kammala biyan kudin kujera ba, duk da mako daya da aka kara musu.
Alhaji Hasan ya ce taron bitar, an shirya shi ne don wayar da kan maniyyata da dole kowane maniyyaci ya halarta, inda ya ce akwai yiwuwar a kwace kujerar wadanda suka
ki halartar bitar.
Da yake tofa albarkacin bakinsa wani wakili a hukumar gudanarwar hukumar a
karamar Hukumar Kurfi, Alhaji Zubairu Ahmad Rawayau ya hori maniyyatan ne su kasance masu nuna halaye na kwarai a lokacin gudanar ayyukansu na Hajji a kasa Mai tsarki.
Shi ma a lokacin da ya je yankin Funtuwa domin kaddamar taron bitar, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Muhammad danyaya Mashi ya ce kimanin mutum 300 ne gwamnatin jihar ta dauki nauyin su domin taimaka wa maniyyata a kasa Mai tsarki.
Shugaban ya ce daga cikinsu akwai malamai masu wa’azi da masu dakon kaya da masu kula da alhazai da kuma wasu daga kananan hukumomin jihar 34 da hedikwatar hukumar. Ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitocin da za su kula da alhazan tun daga nan Najeriya har zuwa Saudiyya.
Sai ya yi kira ga maniyyatan su ba hukumar hadin kan da ya wajaba wajen ganin an samu aikin Hajji mai tsabta, kuma karbabbe.