Jihar Katsina ta fi kowace jiha zaman lafiya – Sarkin Nufawa
Sarkin Nupawan Katsina Alhaji Nda Yunusa Yakubu ya nuna gamsuwa kan yadda ake zaman lafiya a jihar, ind ya ce Katsina ce ke kan gaba a wajen zaman lafiya da lumana a tsakanin al’umma a Najeriya duk da kasancewarta cakude da kabilu da daban-daban.Alhaji Nda Yunusa ya shaida wa Aminiya a ofishinsa cewa, “A Jihar […]

Sarkin Nupawan Katsina Alhaji Nda Yunusa Yakubu ya nuna gamsuwa kan yadda ake zaman lafiya a jihar, ind ya ce Katsina ce ke kan gaba a wajen zaman lafiya da lumana a tsakanin al’umma a Najeriya duk da kasancewarta cakude da kabilu da daban-daban.
Alhaji Nda Yunusa ya shaida wa Aminiya a ofishinsa cewa, “A Jihar Katsina ne kadai ba a samun unguwanni ko wani layi a cikin unguwa ko kasuwa da ake yi wa lakabi da wani yare ko kabilar da suke ba ’yan asalin jihar ba.
Alhaji Nda ya ce, “Duk da cewa kashi 95 na jama’arta Musulmi ne kuma Hausa Fulani, amma da zarar ka ga John za ka tarar suna tare da Hamza, ko beronica na wasa da A’isha ba tare da nuna wani bambanci ba. Kuma mu wadanda ba ’yan asalin jiha ba ba a taba yin wani abu a ce ban da mu ko babu ruwanmu ba. Sama da shekara talatin da nake zaune a Jihar Katsina da labarin da na samu daga magabatanmu, har yanzu ba mu taba gani ko jin inda aka aka yi fadan kabilanci ko addini a duk fadin jihar ba.”
Alhaji Nda ya ce, hatta kudin makaranta da na jarabawa da gwamnatin Ibrahim Shema ke biya wa daliban jihar ba a ware wadanda ba ’yan asalin jihar ba, “Gaskiyar magana Jihar Katsina ta cancanci yabo da zama abin koyi ta fuskoki da dama ga sauran jihohin ksar nan. Kuma ina kira ga jama’a su zauna lafiya domin ciyar da jihar da kasa gaba,” inji shi.