Jihar Kebbi ta kafa Kwamitin Aikin Hajji
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kafa kwamitin mutum 12 kan aikin Hajjin bana a karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim K. Aliyu, Matawallen Yauri.Wannan bayani na kunshe ne a wata takarda dauke da sa hannun Babban Sakataren Labarai na Gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Mu’azu dakingari. Takardar ta bayyana cewa mambobin kwamitin akwai Kwamishinan Ayyuka, Alhaji […]
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kafa kwamitin mutum 12 kan aikin Hajjin bana a karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim K. Aliyu, Matawallen Yauri.
Wannan bayani na kunshe ne a wata takarda dauke da sa hannun Babban Sakataren Labarai na Gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Mu’azu dakingari.
Takardar ta bayyana cewa mambobin kwamitin akwai Kwamishinan Ayyuka, Alhaji Muhammadu Ruwa
dakingari da na Ma’aikatar Al’amuran Masarautu da kananan Hukumomi, Alhaji Rabi’u Muhammad Koko. Sai dan majalisar jihar Alhaji Hassan Muhammad Shalla da Sarkin Fakai Alhaji Muhammadu Hudu danmalam da Shugaban karamar Hukumar Bagudo Alhaji Sama’ila Muhammad Bagudo da na karamar Hukumar Shanga Alhaji Shehu Natsoffi da Alhaji Usman Ankwai Zuru da Alhaji Muhammadu Musa Bayawa da Alhaji Abdullahi Maigandi Yawuri da Alkali Muhammadu Kolado, sai kuma Babban Magatakardar Babbar Kotun Jihar Alhaji Bagudu Bello a matsayin Sakataren Kwamitin.