Jihar Kebbi ta tallafa wa manoma dubu 11 da ambaliya ta shafa
Gwamnatin Jihar Kebbi ta fara rarraba takin zamani ga manoman Jihar dubu 11 da 345 da ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin jihar takwas. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Alhaji Sani Dododo ya bayyana haka lokacin da yake sa ido wajen rarraba wa manoman takin da Gwamnatin Tarayya ta aiko […]
Gwamnatin Jihar Kebbi ta fara rarraba takin zamani ga manoman Jihar dubu 11 da 345 da ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin jihar takwas.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Alhaji Sani Dododo ya bayyana haka lokacin da yake sa ido wajen rarraba wa manoman takin da Gwamnatin Tarayya ta aiko musu da shi don tallafa wa manoman da lamarin ya shafa.
Alhaji Sani Dododo, ya ce ita ma gwamnatin Jihar Kebbi, ta raba buhunan taki masu nauyin Kilo 50 guda dubu 19 da irin shinkafa da sauran kayan aikin gona ga manoma dubu biyu da ke Karamar Hukumar Birnin Kebbi, wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
Shugaban Hukumar ta SEMA, ya nanata cewa, kowane manomi zai samu buhu tara na takin zamani, buhu uku na irin shinkafa da gorunan maganin kwari guda hudu, tare da injin feshi daya, kuma za a rarraba irin rake da ya kudinsu ya kai Naira miliyan biyu, ga manoman rake na kauyukan Karamar Hukumar Shanga da ke jihar.
Ya gargadi wadanda za su ci gajiyar shirin cewa, kada wani ya bai wa wani daga cikin ma’aikatan hukumar na goro don gudun kada su rasa samun kayayyakin. “Duk wanda aka kama da wanda ya ba da da wanda ya karda za a hukunta su,” inji shi.