Jihar Kebbi za ta ba masu kiyon kifi tallafin Naira miliyan 100
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana kudurinta na samar da tallafin Naira Miliyan 100 ga masu sana’ar kiyon kifi, da masu kamun kifi da kuma ‘yan kasuwar masu sana’ar kifi a duk fadin jihar. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Gwamnan jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi a wani taro da gwamnatin jihar Kebbi […]
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana kudurinta na samar da tallafin Naira Miliyan 100 ga masu sana’ar kiyon kifi, da masu kamun kifi da kuma ‘yan kasuwar masu sana’ar kifi a duk fadin jihar.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Gwamnan jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi a wani taro da gwamnatin jihar Kebbi ta shirya domin tattaunawa da kungiyoyin masu sana’ar kiyon kifi, masu kamun kifi da kuma ‘yan kasuwar kifi da ake da su a cikin jihar Kebbi.
An gudanar da taron tattaunawar ne a dakin gudanar da taro na masaukin shugaban kasa da ke Birnin-kebbi. Inda gwamnatin jihar ta tattauna da kimanin mutane dubu biyar daga kananan hukumomi ashirin da daya da ake da su a jihar Kebbi, da suka kunshi masarautun Gargajiya guda hudu na jihar. Haka kuma Sanata Bagudu ya ce, “Gwamnatinsa zata gina makarantu ga ‘ya’yan masunta saboda irin yanayin sana’ar ta masu kamun kifi take”. Ya kuma kara da cewa gwamnatin zata samar da iraruwan kifi na kiyo wanda za’a sanya a cikin gulaben ruwa fadama a dukkan fadin jihar Kebbi domin bunkasa harkar kiyon kifi da kuma kasuwar kifi a jihar. Bugu da kari yace “gwamnatin jihar zata tabbatar da ta samar da babbar kasuwar sayar da kifi a jihar wadda jama’ar kasashen Afirka zasu shigo domin yin kasuwancin sana’ar kifi a jihar”.
Da yake jawabinsa na maraba a wurin taron tun farko, kwamishinan ma’aikatar kiyon Lafiyar Dabbobi na jihar Kebbi, Alhaji Maigari Abdullahi Dakingari ya ce” tun lokacin da gwamnatin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta karbi madafun iko ta bunlo da shirin bayar da tallafi ga Fulani makiyaya da kuma masu kamun kifi don inganta sana’o’insu a jihar ta Kebbi. Ya kuma bayyana cewa a kwanakin baya gwamnatin jihar ta samar da iraruwan kifi na kiyon ga masu sana’ar kiyon kifi iri daban daban a dukkan masarautun gargaji guda hudu da jihar ke da su don bunkasa sana’ar kamun kifi a fadin jihar. Haka kuma manyan mutanen da suka yi jawabi a wurin taron sun hada da shugaban ma’aikatar fadar gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu, Sarkin Shikon Kamba Alhaji Mahmudu Zarumi, Sarkin Kyangan-Kyangakwai Alhaji Suleiman Musa da Sarkin Jirgin Kabi da kuma sauransu.