Jihar Kogi ta rufe asibitoci hudu marasa rijista
Gwamnatin Jihar Kogi ta rufe wasu asibitoci guda hudu bisa laifin aiki ba tare da rijista ba. Biyu daga cikin asibitocin dai a karamar hukumar Adavi suke, daya kuma a garin Lokoja babban birnin jihar, yayin da dayan kuma yake a karamar hukumar Ajaokuta. A cewar jami’in da ya jagoranci rufe asibitocin Dr Stephen Akeh-Oluwarotimi, […]
Gwamnatin Jihar Kogi ta rufe wasu asibitoci guda hudu bisa laifin aiki ba tare da rijista ba.
Biyu daga cikin asibitocin dai a karamar hukumar Adavi suke, daya kuma a garin Lokoja babban birnin jihar, yayin da dayan kuma yake a karamar hukumar Ajaokuta.
A cewar jami’in da ya jagoranci rufe asibitocin Dr Stephen Akeh-Oluwarotimi, tuni suka damka masu asibitocin ga Hedikwatar Hukumar Tsaro ta NSCDC da ke Lokoja.
Oluewarotimi ya ce ko a baya sai da aka taba rufe asibitocin, yana mamakin yadda suka sake maimaita laifin a karo na biyu.
Ya ce matakin rufe asibitocin zai zama izina ga sauran masu aikata makamantan wadannan laifukan da suke jefa rayuwar al’ummar jihar cikin hadari.
Ya kuma ja hankalin al’ummar jihar da su ba su hadin kai wajen yakin, yana mai cewa gwamnatin jihar tana aiki ba dare ba rana wajen kare lafiyar al’ummar jihar.