Jihar Nasarawa ta fara sayar da taki ga manoman rani
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya kaddamar da fara sayar da takin zamani ga manoman rani na bana a jihar. Gwamnan wanda Mataimakinsa, Dokta Emmanuel Akabe ya wakilta ya ce wannan karamci ga manoman jihar shi ne irinsa na farko a tarihinta. Ya ce za a sayar da kowane buhun takin a kan Naira […]
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya kaddamar da fara sayar da takin zamani ga manoman rani na bana a jihar.
Gwamnan wanda Mataimakinsa, Dokta Emmanuel Akabe ya wakilta ya ce wannan karamci ga manoman jihar shi ne irinsa na farko a tarihinta.
Ya ce za a sayar da kowane buhun takin a kan Naira dubu hudu ga manoman domin ba su damar bunkasa aikin noma a jihar.
Ya ce “Idan za a iya tunawa a bara, gwamnatinmu ta sayo tare da raba wa manoman jihar kimanin tan 1,370 na takin a farashi mai rahusa, domin ba su damar samar wa jihar isasshen amfanin gona.”
Sai ya bukaci manoman da za su amfana da takin su tabbatar sun yi amfani da shi yadda ya dace don kwalliya ta biya kudin sabulu musamman samar da wadataccen amfanin gona na noman rani a jihar baki daya.
Tun farko a jawabin Kwamishinan Gona da Albarkatun Ruwa na Jihar, Farfesa Otaki Alanana, ya shawarci manoman jihar su tabbatar sun yi amfani da takin yadda ya kamata ba tare da sayar da shi ba.
Wakilinmu ya gano cewa bayan takin zamani na noman ranin Gwamnatin Jihar ta kuma samar wa manoman wasu nau’o’in iri da ake shukawa da rani don cimma burin wadata jihar da abinci.