Jihar Nasarawa ta mai da almajirai 788 jihohinsu na asali
Gwamnatin jihar Nasarawa a Najeriya ta mayar da almajirai 788 zuwa jihohinsu na asali. Gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule, wanda ya yi sallama da almajiran a wata makarantar sakandare a Lafiya babban birnin jihar ya ce gwamnati ba ta dauki matakin da mummunar manufa ba. Ya ce an cimma wannan matsaya ne a tsakanin gwamnonin […]
Gwamnatin jihar Nasarawa a Najeriya ta mayar da almajirai 788 zuwa jihohinsu na asali.
Gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule, wanda ya yi sallama da almajiran a wata makarantar sakandare a Lafiya babban birnin jihar ya ce gwamnati ba ta dauki matakin da mummunar manufa ba.
Ya ce an cimma wannan matsaya ne a tsakanin gwamnonin jihohin Arewa saboda dakile yaduwar cutar coronavirus.
- Coronavirus: Za a fitar da almajirai 4,443 daga jihar Nasarawa
- Almajirai 16 da aka mayar Kaduna daga Kano suna da Coronavirus
- Coronavirus: Jigawa ta karbi almajirai 524 daga Kano
Gwamna Sule ya kara da cewa an dauki matakin ne saboda mika almajiran ga iyayensu domin su samu kulawa sosai.
Gwamnan ya ce wannan kashin farko ne na almajiran da aka tattara daga kudancin jihar inda ake sa ran za a mika su zuwa jihohin Jigawa, Filato, Kaduna, Gombe da Taraba.
Tun bayan barkewar annobar Coronavirusw asu gwamnonin arewacin Najeriya ke daukar matakin mayar da almajirai jihohinsu na asali.
Jihar Kano ce ta fara daukar irin wannan mataki, lamarin da ya bar baya da kura, domin an samu da yawa daga cikin almajiran da ta mayar Kaduna suna dauke da Coronavirus, kamar yadda gwamnatin Kaduna ta bayyana.