Jihar Neja ta soke ba da kyautar kujerun Hajji

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana soke ba jama’a kyautar kujerun Hajji da aka saba bayarwa duk shekara.Kwamishinan Albarkatun Ruwa kuma shugaban kwamitin da ya duba yadda Hukumar Alhazai ta Jihar ke gudanar da ayyukanta, Alhaji Idris Abubakar Azozo ne ya sanar da haka, inda ya ce kwamitin da Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya […]

Jihar Neja ta soke ba da kyautar kujerun Hajji
Jihar Neja ta soke ba da kyautar kujerun Hajji

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana soke ba jama’a kyautar kujerun Hajji da aka saba bayarwa duk shekara.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa kuma shugaban kwamitin da ya duba yadda Hukumar Alhazai ta Jihar ke gudanar da ayyukanta, Alhaji Idris Abubakar Azozo ne ya sanar da haka, inda ya ce kwamitin da Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya kafa domin bayar da shawarwarin yadda za a gyara al’amuran da suka shafi Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar ne ya gabatar da wannan shawara a matsayin daya daga cikin hanyoyin da za a samu sauki kuma jama’a su gudanar da aikin Hajji cikin sauki. Alhaji Idris Azozo ya ce za a yi wa Hukumar Gudanarwar Hukumar Jin Dadin Alhazan gyaran fuska ta yadda za a mika alhakin gudanar da ita a hannun masana addinin Musulunci da kwararru a fannoni daban-daban domin jan ragamarta domin rage aikata kura-kuran da ake fama da su a shekarun baya.
Shugaban Kwamitin ya ce wakilan kwamitin sun yi nazarin yadda hukumar ke gudanar da al’amuranta, kuma sun yi nazarin rahoton aikin Hajjin bana da Amirul Hajj na Jihar ya gabatar inda suka kara gano yadda kalubalen kula da alhazan jihar a kasa Mai tsarki ke fuskanta.
Ya ce, “Daga cikin sababbin sauye-sauyen da ake so a gabatar a tsarin rabon kujerun zuwa aikin Hajjin, za a rarraba takardun ne a bainar jama’a ta tsarin mai-rabo-ka-samu, inda jama’a za su halarci hedikwatocin kanananan hukumominsu domin shiga cikin tsarin duk wanda ya yi nasara, za a ba shi takardunsa muddin ya biya kudin kujera cikin lokaci.”