Jihar Sakkwato za ta aurar da zawarawa da ’yan mata 250
Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko za ta kashe Naira miliyan 30 wajen aurar da zawarawa da ’yan mata 250, inda zawarawa 125 da ’yan mata 125 za su kasance amare ga samari 125 da kuma zawarawa maza 125.Kwamishinan Jin Dadin Jama’a na Jihar Alhaji Zubairu Yari Goronyo ne ya bayyana […]
????????????????????????????????????

Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko za ta kashe Naira miliyan 30 wajen aurar da zawarawa da ’yan mata 250, inda zawarawa 125 da ’yan mata 125 za su kasance amare ga samari 125 da kuma zawarawa maza 125.
Kwamishinan Jin Dadin Jama’a na Jihar Alhaji Zubairu Yari Goronyo ne ya bayyana haka a wurin tantance wadanda za a aurar karo na karshe da aka aiwatar a babban dakin taro na gidan tarihi na Waziri Junaidu da ke Sakkwato.
Alhaji Zubairu ya ce wannan tantancewa ita ce ta karshe kuma da zarar an kammala ta za su fadi ranar da za a taru domin daurin auren a Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi ko Gidan Gwamnati ko Babban Masallacin Juma’a na Sakkwato.
Ya ce gwamnati za ta dauki nauyin biyan sadakin kowace mace da aka yanke a kan Naira dubu 20 da saya mata gado daya da kujeru da labulen daki da tukunyar girki da buta da turmin atamfa biyu, inda maza za a ba kowanenu shadda yadi goma da Naira dubu 20 ya ja jari.
“Kuma za mu yi kwamitin da zai rika kula mana da halin da ma’auratan suke ciki,” inji Kwamishinan.
Alhaji Yari Goronyo ya ce gwamnati ta bullo da wannan shiri ne domin tallafa wa matasa marasa karfi da rage yawan mata marasa aure, kuma idan wannan bikin da za su fara ya yi armashi, to za su rika yin sa duk bayan wata uku.
Shugaban kungiyar hada auren na Jihar Sakkwato wadanda su ne suka nemi gwamnatin jihar ta shiga cikin lamarin don inganta shirin Alhaji Bello kofar Rini ya gode wa gwamnatin kan wannan kokari da take yi, kuma ya ba da tabbacin ba za su yarda da duk wani batagari da zai zo domin kawo matsala ga lamarin ba. Ya ce, duk da an yanke kudin da suka ce za su kashe daga Naira miliyan 80 zuwa Naira miliyan 30 suna godiya da wannan hobbasa.