Jihar Yobe na da ’yan gudun hijira dubu 135 – Bego

Jihar Yobe tana fama da ’yan gudun hijira kimanin mutum dubu 135 da 511 da ke zaune a sassan kananan hukumomi  13 da ke jihar, sakamakon raba su da muhallinsu da rikicin Boko Haram ya yi.Daraktan Harkokin ’Yan jarida da Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Alhaji Abdullahi Bego ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema […]

Jihar Yobe na da ’yan gudun hijira dubu 135 – Bego
Jihar Yobe na da ’yan gudun hijira dubu 135 – Bego

Jihar Yobe tana fama da ’yan gudun hijira kimanin mutum dubu 135 da 511 da ke zaune a sassan kananan hukumomi  13 da ke jihar, sakamakon raba su da muhallinsu da rikicin Boko Haram ya yi.
Daraktan Harkokin ’Yan jarida da Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Alhaji Abdullahi Bego ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a Damaturu, inda ya ce gwamnatin jihar tana bakin kokarinta don ganin ta ba da kula ta musamman ga ’yan gudun hijirar musamman ta hanyar samar musu da wuraren da za su tsuguna da kayan abinci da suturu da sauran kayan kyautata rayuwarsu.
Ya ce baya ga kula da ’yan hijirar kuma har wa yau gwamnatin ta kuma kashe kusan Naira biliyan 12 kan abin da ya shafi inganta jin dadin jami’an tsaron da ke kula da jihar inda duk da wadannan makudan kudi da ta kashe kan tsaron Naira miliyan 150 ne kacal Gwamnatin Tarayya ta tallafa da su.
Kakakin Gwamnan ya ce gwamnatin ta kuma ba da tallafin sama da Naira miliyan 61 ga ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyinsu sanadiyar hare-haren kungiyar Boko Haram. Sai ya ba da tabbaci ga al’ummar jihar cewa babban kudirin gwamnatin a yanzu shi ne fuskantar manyan kalubalen da suka hada da ilimi da kiwon lafiya da a yanzu za ta mayar da akalarta a kansu.