Jihar Yobe ta kasafta kusan Naira biliyan 89

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya mika wa Majalisar Dokokin Jihar kasafin bana, inda ya ce jihar tana sa ran kashe Naira biliyan 88 da miliyan 900.Da yake gabatar da kasafin a gaban majalisar, Gwamna Gaidam ya ce kasafin kudi an yi masa lakabi ne da “Kasafin Kudin keke-da-keke, Raya kasa da Dogaro da […]

Jihar Yobe ta kasafta kusan Naira biliyan 89
Jihar Yobe ta kasafta kusan Naira biliyan 89

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya mika wa Majalisar Dokokin Jihar kasafin bana, inda ya ce jihar tana sa ran kashe Naira biliyan 88 da miliyan 900.
Da yake gabatar da kasafin a gaban majalisar, Gwamna Gaidam ya ce kasafin kudi an yi masa lakabi ne da “Kasafin Kudin keke-da-keke, Raya kasa da Dogaro da kai.”
Gwamnan ya ce kasafin yana kunshe da muhimman kudirorin da suka kunshi kokarin raya kasa da fafitukar samo hanyoyin bi don hako ma’adinan da ke jihar don dogaro da kai ganin kasuwar man fetur da tattalin arzikin kasar nan ya dogara da ita ta fadi.
Ya ce an kebe Naira biliyan 18 ga Ma’aikatar Ayyuka da Hanyoyi, yayin da Ma’aikatar Ilimi ta samu fiye da Naira biliyan 17.
Da yake karbar kundin kasafin, Shugaban Majalisar Jihar Alhaji Adamu Dala Dogo ya ba da tabbaci ga Gwamnan da al’ummar jihar cewa majalisar za ta gaggauta duba kasafin tare da rattaba hannu a kai ba tare da bata lokaci ba don su gudanar da ayyukan raya jihar.