Jihar Yobe ta samar da gidaje ga malaman makaranta
Gwamnatin Jihar Yobe ta gina gidaje ga malaman makarantun firamare a dukanin kananan hukumomin jihar 17 don inganta yanayin koyarwa a jihar.Kwamishinan Ilimi na Jihar, Alhaji Muhammad Lamin ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke garin Damaturu.Kwamishina Muhammad Lamin ya ce, gwamnatin ta yi haka ne a kokarin da take yi […]
Gwamnatin Jihar Yobe ta gina gidaje ga malaman makarantun firamare a dukanin kananan hukumomin jihar 17 don inganta yanayin koyarwa a jihar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Alhaji Muhammad Lamin ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke garin Damaturu.
Kwamishina Muhammad Lamin ya ce, gwamnatin ta yi haka ne a kokarin da take yi na ceto ilimi daga tabarbarewar da yake yi tare da karfafa wa malaman makarantar karfin gwiwa domin zuwa duk inda aka tura su, ba tare da taraddadin samun masauki ba musamman a yankunan karkara.
Kwamishinan ya ce, a halin da ake ciki, gwamnatin ta bullo da kyakkyawan kudiri dangane da habaka ilimin ’ya’ya mata wanda hakan na daga cikin dalilan da suka sa suka fara samar da gidajen kwana ga malaman.
Alhaji Muhammad Lamin ya ce, jarin da gwamnatin jihar ke zubawa a harkokin ilimi musamman ilimin sakandare ya fara samar da kyakkyawan sakamako ganin cewa, daliban jihar da ke kammala makarantun sakandare na samun sakamakon da ke ba su da damar shiga manyan makarantu don karo ilimi.
Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin za ta ci gaba da bayar da gudunmawa ga harkokin ilimi don samar da kwararrun ma’aikatan da za su gudanar da harkokin jihar.