Jihar Yobe ta sha alwashin inganta koyarwa a makarantunta

Gwamnatin Jihar Yobe na aiki sau da kafa don habaka harkokin koyo da koyarwa  a makarantun jihar domin farfado da ilimi daga tabarbarewar da rashin zaman lafiya ya jefa shi a ciki.Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ne ya bayyana haka a ganawarsu da Aminiya a Damaturu, inda ya cewar duk da halin da […]

Jihar Yobe ta sha alwashin inganta koyarwa a makarantunta
Jihar Yobe ta sha alwashin inganta koyarwa a makarantunta

Gwamnatin Jihar Yobe na aiki sau da kafa don habaka harkokin koyo da koyarwa  a makarantun jihar domin farfado da ilimi daga tabarbarewar da rashin zaman lafiya ya jefa shi a ciki.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ne ya bayyana haka a ganawarsu da Aminiya a Damaturu, inda ya cewar duk da halin da jihar ta samu kanta a ciki a sama da shekara biyu sakamakon tabarbarewar tsaro wanda ya haifar da kone makarantun firamare da sakanadare da na gaba da sakandare da kuma kashe dalibai da malamai, gwamnatin ta tashi tsaye don ganin lamuran ilimi sun inganta a dan abin da ke saura na daunin da ake ba ta daga asusun tarayya.
 Alhaji Muhammad Lamin ya ce ma’aikatarsa ta dauki malamai sama da dubu hudu masu takardun diploma da makamantansu, ta horar da su dabarun koyarwa don koyarwa a makarantun firamare da kananan sakandaren jihar a matsayin kawar da zaman kashe wando da matasan ke yi da kuma samar da kwararrun malamai.
 Ya ce a kowane lokaci gwamnatin jihar na shirya tarurrukan bita ga malaman makarantun a kokarin da ake yi na cika burin muradun karni wajen inganta ilimi cikin lokacin.
Kwamishinan ya ba da tabbaci ga malaman makarantun cewa gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin ta kula da hakkokinsu, ya kuma hori malaman su rika kokarin sauke nauyin da ke kansu wajen koyar da yaran abin da ya kamata tare da kauce wa halayyar nan ta kin zuwa wurin aiki ko barin wurin aiki ba tare da izni ko dalili mai karfi ba.