Jihar Yobe za ta horar da sababbin malamai dubu uku a karkashin NTI
Gwamnatin Jihar Yobe ta ce ta shirya don daukar nauyin sababbin malaman makaranta da ta dauka aiki su 3000 don samun horo a Cibiyar Malamai ta kasa (NTI) a kokarin da take yi na samar da ilimi mai inganci ga yaran jihar.Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da […]

Gwamnatin Jihar Yobe ta ce ta shirya don daukar nauyin sababbin malaman makaranta da ta dauka aiki su 3000 don samun horo a Cibiyar Malamai ta kasa (NTI) a kokarin da take yi na samar da ilimi mai inganci ga yaran jihar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu, inda ya ce, adadin malaman da gwamnatin jihar ta dauka da yawansu ya kai dubu uku ta yi haka ne domin fuskantar kalubalen da jihar ke ciki na tabarbarewar ilimi da kuma burin gwamnatin jihar na ganin lamarin ya zama tarihi a kokarinta na ganin jihar ta shiga sahun jihohin kasar nan da ke gaba wajen ci gaba a harkokin ilimi.
Kwamishina Lamin ya ci gaba da cewa daukar wannan mataki na horar da sababbin malaman ya zama dole ne, saboda galibinsu ba su da kwarewa a aikin malanta, don haka ba zai yiwu a koyar ba tare da mutum ya samu horo a kan aikin koyarwa ba.
Ya ce bayan horar da malaman da gwamnatin ke yi har ila yau gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Ibrahim Gaidam ta daura damarar shawo kan barazanar da harkokin ilimi ke fuskanta ta fannin tsaro, sakamakon yadda ake kai wa makarantun jihar hare-hare.
Kwamishinan ya hori sababbin malaman su dukufa wajen samun horon ta yadda za su samu damar koyar da daliban jihar kamar yadda tsarin ilimi na kasa ya tanada.