Jihar Yobe za ta kashe Naira biliyan 16 kan hanyoyi

Gwamnatin Jihar Yobe ta ware kimanin Naira biliyan 16 don gina hanyoyin mota a bangarori n jihar da nufin samar al’umma sauki wajen tafiye-tafiye da safarar amfanin gonarsu cikin sauki.Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ne ya bayyana haka a yayin da yake kaddamar da aikin hanyar Damaturu zuwa Buni-Gari ta wuce Magza da ke da […]

Jihar Yobe za ta kashe Naira biliyan 16 kan hanyoyi
Jihar Yobe za ta kashe Naira biliyan 16 kan hanyoyi

Gwamnatin Jihar Yobe ta ware kimanin Naira biliyan 16 don gina hanyoyin mota a bangarori n jihar da nufin samar al’umma sauki wajen tafiye-tafiye da safarar amfanin gonarsu cikin sauki.
Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ne ya bayyana haka a yayin da yake kaddamar da aikin hanyar Damaturu zuwa Buni-Gari ta wuce Magza da ke da iyaka da Jihar Borno mai tsawon kilomita 77 da aka ba Kamfanin RRC kan Naira biliyan biyar da miliyan 999 da dubu 210 tare da wa’adin kammala ta a cikin wata 24.
Gwamna Gaidam ya ce duk da cewa hanyar ta Gwamnatin Tarayya ce amma saboda muhimmancin da ta ke da shi ga al’ummar jihar ya zama wajibi su sake gina ta, kasancewar Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da ita.
Ya ce tun a farkon shekarun 1970 aka gina hanyar amma har zuwa yau ba ta sake waiwayarta da nufin gyara ba ballantana ta yi tunanin gina sabuwa.
Gwamnan ya ce kowa ya san irin azabar da al’ummomin yanki ke sha game da hanyar kuma ne ya sa gwamnatinsa ta yanke shawarar gina hanyar da ke a bangarenta don tallafa wa al’ummarta.
Ya nemi al’ummar jihar su ci gaba da addu’ar zaman lafiya mai dorewa a jihar domin kuwa Allah Yana tare da duk wadanda aka zalunta.