Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet

Mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3.

Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet

Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu.

Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga ƙarfe 12 zuwa ƙarfe 3 na rana.

Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar.

Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Kogi da Nasarawa da kuma Benue.

Sauran sun haɗa da Enugu da Anambra da Abia da Ebonyi da Cross River da birnin tarayya Abuja.

NiMet ta ce wasu jihohin da ka iya fuskantar wannan barazana sun haɗa da Taraba da Adamawa da Filato da Kaduna da Zamfara da kuma Sakkwato.

Ta kuma shawarci al’umma da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin – su kuma yi amfani da fanka da na’urar sanyaya ɗaki da kuma zama a wurare masu inuwa.

Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa

Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa

Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi

Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato