Jihohi 14 na iya fuskantar ambaliyar ruwa — NiMet

NEMA ta ce ya zama wajibi al’ummomin da ke cikin haɗarin ambaliya su ɗauki matakan kariya tun kafin lamarin ya ta’azzara.

Jihohi 14 na iya fuskantar ambaliyar ruwa — NiMet

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa jihohi 14 na ƙasar na iya fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin ranakun 14 zuwa 20 ga watan Yuli, sakamakon mamakon ruwan sama da ake hasashen zai sauka a wasu sassan ƙasar.

A cikin hasashen da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa jihohin Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Benuwe, Borno, Cross River, Edo, Enugu, Imo, Kaduna, Legas, Neja da Filato ne ke cikin jerin waɗanda ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa.

NiMet ta buƙaci mazauna yankunan da abin zai iya shafa su ɗauki matakan kariya, musamman ta hanyar guje wa zama ko zirga-zirga a wuraren da ke da tarihin ambaliya, tare da bin duk wani umarni daga hukumomin da abin ya shafa.

A nata ɓangaren, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta shawarci al’ummomin da ke cikin yankunan da ke fuskantar haɗarin ambaliya da su yi biyayya ga gargaɗin da aka fitar, su kuma ƙaura zuwa wuraren da ba sa cikin haɗari domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Darakta Janar ta NEMA, Zubaida Umar ce ta yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da Sashen Yaɗa Labarai na hukumar ya fitar a ranar Asabar, inda ta ce ya zama wajibi al’ummomin da ke cikin haɗarin ambaliya su ɗauki matakan kariya tun kafin lamarin ya ta’azzara.

NEMA ta ce ɗaukar matakan kariya tun da wuri zai taimaka wajen rage asarar rayuka da dukiyoyi yayin da damina ke ƙara ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar.