Jihohi 15 sun gudanar da Gasar Dambe a Jihar Adamawa

Ma’aikatar Wasanni ta Jihar Adamawa ta ce akalla jihohi 15 ne suka fafata a gasar wasan dambe a jihar. A bara ce aka sanya wasan dambe a cikin gasar wasanni a birnin Abuja inda dambe ya shiga cikin wasannin da za a rika yi a tsakanin jihohi. Shugaban Kungiyar ’Yan Damben Jihar Adamawa, Alhaji Adamu […]

Jihohi 15 sun gudanar da Gasar Dambe a Jihar Adamawa

Ma’aikatar Wasanni ta Jihar Adamawa ta ce akalla jihohi 15 ne suka fafata a gasar wasan dambe a jihar.

A bara ce aka sanya wasan dambe a cikin gasar wasanni a birnin Abuja inda dambe ya shiga cikin wasannin da za a rika yi a tsakanin jihohi.

Shugaban Kungiyar ’Yan Damben Jihar Adamawa, Alhaji Adamu Mu’azu ya bayyana wa Aminiya cewa mutum 40 ne suka yi shiga gasar daga jihohi 15 na Arewa.

“Mun gudanar da wannan wasa ne domin samun hadin kai a tsakanin masu gudanar da wasannin dambe wadanda yawancinsu matasa ne kuma daga jihohin Arewa,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “Wannan gasar mun gudanar da ita ce domin shirya masu wasan don fafatawa a babbar gasa ta kasa wadda ake kira da “Edo 2020” da za a fara daga gobe.

Misis Esther Dominic wadda ita ce Daraktar Rikon Kwarya ta Hukumar Wasanni ta Jihar ta ce, ta yi matukar farin ciki ganin yadda aka sanya wasan dambe a cikin wadanda za su fafata a gasar wasanni ta kasa.

Ta kara da cewa gwamnatocin jihohi sun sanya wasan dambe a cikin wasannin da za a rika yi domin tace ’yan wasan da za su wakilce su a gasar wasanni ta kasa ta “Edo 2020” wadda ake sa ran za a yi ta a watan Maris.

“Mun gudanar da wannan wasa ne domin samo wadanda suka kware a wasan dambe domin su kasance cikin wadanda za su je gasar ‘Edo 2020’ a Jihar Edo,” inji ta.

Ta ce za su rika shiga kauyuka domin nemo wadanda suka kware a wannan harka don a ba su damar fito da kwararru da za su ciyo kofi ga Jihar Adamawa a duk lokacin da aka gudanar da gasar.

Jihohin Adamawa da Taraba da Gombe da Kaduna da Borno da Yobe da Kano da Jigawa da Kebbi da Filato da Neja da Katsina da Sakkwato da Zamfara da kuma Kogi na daga cikin wadanda suka fafata  a wasannin a Jihar Adamawa.