Jihohi 19 da ke cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa
Daga yanzu zuwa ƙarshen watan Yuli, ƙasar na iya fara fuskantar ambaliyar ruwan da za ta yi gagarumar barna.
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa za a fara samun ambaliyar ruwa daga ƙarshen watan Yuli, inda ta ce jihohi 19 da babban birnin tarayya Abuja suna cikin haɗari.
Gwamnati ta kuma yi gargaɗin cewa ci gaba da smun ambaliya na iya ƙara ta’azzara cutar kwalara da ta addabi wasu jihohi a halin yanzu.
- Binciken Ganduje: Kotu ta ba shugabannin kwamiti awa 48 su sauka
- An kama ’yan bindiga 5 bayan musayar wuta da ’yan sanda a Abuja
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ya zuwa ranar Laraba, Hukumar Yaƙi da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), ta ce cutar kwalara ta yi sanadiyar mutuwar mutane 63 da kuma wasu 2,102 da ake zargin sun kamu da cutar.
Da yake yi wa manema labarai jawabi kan matsalar ambaliyar ruwa a ƙasar, a ranar Alhamis, Ministan Ruwa da Tsaftar Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ya ce matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta tun cikin wata Mayun da ya gabata ta haɗa har da birane.
Ministan ya alaƙanta matsalar da mamakon ruwan sama da ake samu a daminar bana, da rashin inganci da toshewar magudanan ruwa a cikin birane.
Ya ce daga yanzu zuwa ƙarshen watan Yuli, ƙasar na iya fara fuskantar ambaliyar ruwa, wanda zai yi mummunar ɓarna.
Ya bayyana jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar da suka haɗa da Akwa Ibom da Anambra da Benuwe da Bayelsa da Kuros Ribas da Delta da Edo da Jigawa da Kogi.
Sauran jihohin sun haɗa da: Kebbi da Kaduna da Neja da Nasarawa da Ondo da Ogun da Ribas da Taraba da kuma babban birnin tarayya Abuja
Ministan ya ce dole a yi shirin ko ta kwana na fuskantar ambaliyar ruwa la’akari da yadda Kogin Neja ke ƙara tumbatsa, wanda da zarar magudanan ruwa ta sun cika za a samu ambaliya.
Dangane da halin da ake ciki a madatsar ruwa ta Lagdo a Kamaru, Ministan ya ce masu gudanar da aikin samar da wutar lantarki sun sanar da cewa a halin yanzu suna cike madatsar ruwan.
Game da abin da gwamnatin tarayya ke yi na daƙile ambaliya da ake samu a duk shekara sakamakon sako ruwa daga madatsar ruwa ta Lagdo, Ministan ya ce an kusa kammala shirye-shiryen na gina wasu madatsun ruwa daban-daban.
Ya ce an tsara taswirar waɗannan madatsun ruwa, kuma gwamnati ta kusa aiwatar da yin aikin.
A fannin cutar kwalara, Ministan ya yi gargaɗin cewaƙaruwar ambaliyar ruwa na iya ƙara tsananta annobar, inda ya ce an kafa wani kwamitin daga fadar shugaban ƙasa domin ganin yadda za a shawo kan matsalar.