Jihohi 20 da suka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi

Kimanin jihohi 20 ne suka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ko kuma za su fara biya daga wannan makon. Bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin ƙwadago, an amince da ƙara mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000. Tattaunawar wadda aka shafe tsawon lokaci ana yin ta, ta haifar da […]

Jihohi 20 da suka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi

Kimanin jihohi 20 ne suka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ko kuma za su fara biya daga wannan makon.

Bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin ƙwadago, an amince da ƙara mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000.

Tattaunawar wadda aka shafe tsawon lokaci ana yin ta, ta haifar da samar da ƙudirin doka wacce Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da ita, inda shi kuma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu a kai ta zama doka a ranar 29 ga watan Yuli.

Kwamitin daidaitawa da Gwamnatin Tarayya ta kafa ya gabatar da rahotonsa na ƙarshe a kan ƙa’idojin da za a bi.

Kwamitin ya kasance ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (HCSF) Misis Esther Walson-Jack.

Tuni Gwamnatin Tarayya ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin bayan tattaunawa da shugabannin ƙwadago.

Su ma jihohi sun fara bayyana tsarin biyan sabon mafi ƙarancin albashin ga ma’aikatansu.

Sai dai kuma aiwatar da shi ya zama jidali a faɗin jihohin ƙasar, inda har yanzu wasu ba su kama hanyar biya ba.

A gefe guda kuma, a yayin da wasu jihohin suka amince da biyan N70,000 ɗin, wasu kuma sun sha alwashin biyan sama da hakan.

Wannan rahoto ya yi duba kan jihohin da suka amince da biyan N70,000 da waɗanda suka ce za su biya sama da hakan.

Masu biyan sama da N70,000

Legas

A ranar 16 ga watan Oktoban Gwamnan

Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da sabon albashin mafi ƙanƙanta, inda ya ce za su fara biyan Naira 85,000.

Hakan na nufin ƙarin Naira 15,000 kan abin da Gwamnatin Tarayya ta ƙayyade. Kazalika, gwamnan ya ce, yana fatan gwamnatinsa za ta ƙara albashin zuwa Naira 100,000 nan da watan Janairun 2025, “saboda tsadar rayuwar da ake ciki”.

Ribas

Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas ma ya ayyana Naira 85,000 a matsayin albashin mafi ƙanƙanta a jihar. Ya sanar da hakan ne a ranar 18 ga watan Oktoba.

Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta amince da biyan Naira 80,000 ga ma’aikatata, kamar yadda Gwamana Mohammed Umaru Bago ya sanar a ranar 25 ga watan Oktoba.

Ogun

Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun shi ma ya amince da biyan Naira 77,000, kamar yadda wata sanarwa daga sakataren gwamnatin jihar ta nuna a ranar 15 ga watan Oktoba.

Kebbi

A ranar 23 ga watan Oktoba kuma,

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya amince da biyan Naira 75,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan jihar.

Ondo

Jihar Ondo ma ta bi sawun takwarorinta, inda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya sanar da biyan Naira 73,000 ga ma’aikatan jihar a matsayin albashi mafi ƙaranci.

Sanarwar tasa ta zo ne yayin da ake shirin gudanar da zaɓen gwamnan jihar a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kogi

Gwamnan Kogi, Usman Ododo ya amince da biyan Naira 72,500 a matsayin mafi ƙarancin albashi a jihar.

Wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook ta ce, gwamnati ta soke biyan haraji a kan sabon albashin na shekara ɗaya.

Gombe

A Jihar Gombe kuwa, gwamnati da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago sun saka hannu kan yarjejeniya a ranar 14 ga watan Oktoba da zimmar ɗaga albashin mafi ƙanƙanta zuwa Naira 71,451.

Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da biyan Naira 71,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta da za ta biya ma’aikatanta.

Bayan ganawa da wakilan ƙungiyar ƙwadago a ranar Talata 29 ga watan Oktoba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwamba, wanda zai ƙara yawan albashin da gwamnatin ke biya da Naira biliyan shida a matakin jiha da kuma Naira biliyan bakwai a matakin ƙananan hukumomi.

Gwamnan, ya ƙara da cewa, ƙarin da aka yi wa malamai 20,737, ya sa an samu ƙarin Naira miliyan 340 a albashinsu.

Masu biyan N70,000

Anambra

Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma

Soludo ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta fara biyan Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi daga watan Oktoban 2024.

Jigawa

A ranar 25 ga watan Oktoba Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya sanar da amincewa da biyan Naira 70,000 a gidan gwamnati, jim kaɗan bayan ya karɓi rahoton kwamatin da ya kafa kan mafi ƙanƙantar albashin.

Katsina

Shi ma Gwamnan Katsina, malam Dikko Radda ya ce, gwamnatinsa na shirin fara biyan Naira 70,000 ɗin a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.

Ebonyi

Tun a watan Satumba ne kuma Gwamnatin Jihar Ebonyi ƙarƙashin jagorancin Francis Nwifuru ta amince da biyan Naira 70,000 ga ma’aikatan jihar.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na cikin na farko-farko da suka sanar da amincewa da Naira 70,000 tun a watan Agusta – wata ɗaya bayan saka wa sabuwar dokar hannu.

Oyo

Shi ma Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta fara biyan Naira 70,000 da zarar an daddale maganar ƙarin albashin baki ɗaya.

Borno

Gwamnatin Jihar Borno ta ce, za ta fara biyan Naira 70,000 daga watan Oktoban 2024.

Binuwai da Osun

Su ma jihohin Osun da Binuwai sun bayyana aniyarsu ta fara biyan sabon albashin mafi ƙanƙanta.

Waɗanda suke kan tattauanwa

Har yanzu akwai jihohin da ba su kai ga cim ma matsaya ba game da biyan Naira 70,000 ko sama da haka ba.

Sun ƙunshi Zamfara da Akwa Ibom da Bayelsa.