Jihohi 21 na neman bashin N1.65trn duk da ƙaruwar kuɗaɗen tarayya da 40%
Sun ce za su yi amfani da bashin tiriliyan N1.65 da suke neman fitowa ne wajen cike giɓin da suka samu a kasafin kuɗinsu na shekarar 2024 da muje ciki.
Jihohi 21 a Najeriya na neman ciyo bashin Naira tiriliyan daya da biliyan 650, duk kuwa da ƙarin kashi 40% da aka samu kuɗaɗen da suka samu daga Kwamitin Asusun Tarayya (FAAC) a shekara guda da ta gabata.
Bincike ya nuna cewa kashi 20% na kuɗaɗen FAAC na watan Yuni 2023 kaɗai (biliyan N160) zai gina cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 320 a faɗin Najeriya.
Aminiya ta gano cewa tuni jihohin suka aike da takardunsu na neman ciyo bashin daga ƙasashen waje da kuma cikin gida. Ragowar jihohin kuma ba su bayyana nasu ba, game da ciyo bashi ko akasin haka.
Ga jerin jihohin da yawan bashin da kowaccensu ke neman ciyowa:
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ya Kamata Alaka Ta Kasance Tsakanin ‘Yan Sanda Da Al’umma
- Kotu ta tsare matashi kan sukan Gwamnan Sakkwato da matarsa
- Adamawa – Biliyan N68.46.
- Anambra – Biliyan N245.
- Bauchi – Biliyan N59.08.
- Bayelsa – Biliyan N64.
- Benue – Biliyan N34.69.
- Borno – Biliyan N41.71.
- Ebonyi – Biliyan N20.5.
- Edo – Biliyan N42.71.
- Ekiti – Biliyan N27.15.
- Jigawa – Biliyan N1.78.
- Kaduna – Biliyan N150.1.
- Kebbi – Biliyan N36.7.
- Katsina – Biliyan N163.87.
- Kogi – Biliyan N37.08.
- Kwara – Biliyan N30.76.
- Osun – Biliyan N12.36.
- Oyo – Biliyan N133.4.
- Nasarawa – Biliyan N32.93.
- Gombe – Biliyan N73.75.
- Enugu – Biliyan N103.
- Imo – Biliyan N271.34.
Gwamnatocin jihohi 21 da ke neman wannan bashin na Naira tiriliyan 1.65 sun ce za su yi amfani da kuɗaɗen ne wajen cike giɓin da suka samu a kasafin kuɗinsu na shekarar 2024 da muje ciki.
Daga watan Yunin 2023 zuwa 2024, jihohi 36 da ƙananan hukumomi 7774 da ke Najeriya da Birnin Tarayya sun samu jimillar Naira tiriliyan bakwai da biliyan 600 daga Asusun Tarayya.
Hakan ya muna an samu ƙarin kuɗaɗen shiga da ake rabawaa a FAAC daga lokacin da Shugaba Tinubu ya janye tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, ranar da ya karɓi mulki.
Hakazalika bayanan da Aminiya ta samu na hasashen kuɗaɗen da jihohi za su samu daga FAAC a 2024 zai kai Naira tiriliyan biyar da biliyan 540, wanda ya zarce tiriliyan 3 da biliyan 300 da suka samu a 2023.
A ƙarƙashin sabon tsarin rabon kuɗaɗen shiga na FAAC, Gwamnatin Tarayya banda kaso 52.68%, jihohi na da kashi 26.72% sai ragowar kashi 20.60% na ƙananan hukumomi.
Da waɗannan kuɗaɗen shiga na tarayya da kuma waɗanda kowane matakin gwamnati ke tara wa kansa, ake sa ran gwamnatoci su yi amfani da su wajen sauke nauyin al’umma da ya rataya a wuyansu.
A ranar 11 ga watan Yuni dai FAAC ta tura wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu ne zuwa asusunsu gwamnatocin jihohi kai-tsaye.
Ana iya tuna cewa a watan Yuli Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin tabbatar da ’yancin cin gashin kan gudanar da kuɗaɗe ga ƙananan hukumomi 774 da ke Najeriya.
Kotun Ƙoli ta ce haramun ne abin da gwamnatocin jihohi ke yi na ƙarba, ajiyewa da kuma gudanar wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu.
Don ta ba da umarnin daga lokacin a riƙa sanya wa ƙananan hukumomin duk kuɗaɗensu kai-tsaye a cikin asusunsu.
Daga watan Yunin 2023 zuwa 2024 dai kuɗaɗen FAAC da jihohi da ƙananan hukumomi suka samu sun ƙaru da kashi 40%, zuwa tiriliyan N7.6.
Kuɗaɗen FAAC da jihohi da ƙananan suka samu a 2023.
– Yuni: Jihohi, N299.92bn; ƙananan hukumomi, N221.79.
– Yuli: Jihohi, N310.670bn, ƙananan hukumomi, N229. 409.
Agusta: Jihohi, N319.52 billion; ƙananan hukumomi, N236.23bn.
– Satumba: Jihohi, N361.19bn; ƙananan hukumomi, N266.54b.
– Oktoba: Jihohi, N287.07bn; ƙananan hukumomi, N210.90bn.
– Nuwamba: Jihohi, N379.41bn; ƙananan hukumomi, N278.04bn.
– Disamba: Jihohi, N396.693bn; ƙananan hukumomi, N288.928 bn.
Kason 2024
– Janairu: Jihohi N379.407bn; ƙananan hukumomi, N278.041bn.
– Fabrairu: Jihohi, N366.95bn; ƙananan hukumomi, N267.15bn.
– Maris: Jihohi, N398.689bn; ƙananan hukumomi, N288.688bn.
– Afrilu: Jihohi, N403bn; ƙananan hukumomi, N293bn.
-Mayu: Jihohi, N388.419bn; ƙananan hukumomi, N282.476bn.
– Yuni: Jihohi, N461.979bn; ƙananan hukumomi, N337.019bn.
Hauhawar harajin VAT
Kuɗaɗen harajin sayen kaya (VAT) sun ƙaru da kashi 228.% zuwa Naira tiriliyan 2.42 a watanni biyar na farkon shekarar 2024, daga Naira biliyan 736 da miliyan 60 a watanni biyar na farkon 2023.
Ladar Haƙo ɗanyen mai
Hakazalika kaso 13% na kudaden da ake ba wa jihohin da ake haƙo ɗanyen mai ya ƙaru da kashi 234% zuwa biliyan 519.83 a watanni biyar na farkon 2024, idan aka kwatanta da biliyan 155.5 da aka samu a irin lokacin a 2023.
20% na kuɗaɗen Yuni zai gina asibiti ci 320.
Kuɗaɗen FAAC da aka raba wa matakan gwamnati uku a watan Yuni 2024, ya kai Naira tiriliyan ɗaya da biliyan 300.
Bisa kiyashin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Naira miliyan 500 ya isa a gina cibiyar lafiya a matakin farko.
Bisa wannan lissafi, kashi 20% na kuɗaɗen FAAC na watan Yuni kaɗai (biliyan N160) zai gina cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 320 a fadin Najeriya.