Jihohi 36 sun maka Buhari a kotu

Jihohi 36 na Najeriya sun maka gwamnatin tarayya kotun koli domin ta janye umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rataba wa hannu kan su cigaba da kashe kudadensu wajen kula da kotuna. A ranar 22 ga watan Mayun 2020 ne dai shugaban kasa Muhammadu ya rattaba wa umurnin mai Lamba: 00-10-2020 hannu. ‘Najeriya ta […]

Jihohi 36 sun maka Buhari a kotu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Jihohi 36 na Najeriya sun maka gwamnatin tarayya kotun koli domin ta janye umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rataba wa hannu kan su cigaba da kashe kudadensu wajen kula da kotuna.
A ranar 22 ga watan Mayun 2020 ne dai shugaban kasa Muhammadu ya rattaba wa umurnin mai Lamba: 00-10-2020 hannu.
Kwamishinonin shari’ar jihohi ne suka shigar da karar, inda shi kuma ministan Shari’a tilo zai kare gwamnatin tarayya.
A takardar karar da Lauyansu, Austin Alegeh (SAN) ya shigar a ranar 16 ga watan Satumbar 2020, Gwamnonin sun bukaci kotu ta tursasa gwamnatin tarayya ta mayar wa ko wacce jiha kudaden da ta kashe wajen kula da gine-gine a kotuna da suka hada da kotunan daukaka kara da manyan kotunan da kotunan Shari’a a jihohinsu.
Jahohin sun kalubalanci umurnin da shugaban kasa ya bayar kan cewa ya saba wa sashe na 6 da 8(3), da sakin layi na 21(e) na bangare na uku a kudin tsarin mulki na 1999, wanda ya tilasta gwamnatin tarayya ta “Rinka daukar nauyin kashe kudin zahiri da na hadin gwiwa da jihohi a kotunan koli da kotunan daukaka kara da kotunan Shari’a da manyan kotuna, wadanda aka kirkira karkashin sashe na 6 kundin tsarin mulkin kasa.
Sai dai ya zuwa yanzu kotun ba ta sa lokacin fara sauraron karar ba.