Jihohi sili da manuniyar sama

Batutuwa na bazuwa a kasar Haurobiya cewa jihohi sili da manuniyar sama babu tsaro a cikinsu, sai dai tsoro, kuma tushen wannan batu an ce ya fito ne daga kasar Uban-mama, wato Amari-kowa. Akwai al’amura kramin lauje, wato ko dai Amurkawa na son falla mana mari, su sanya kow aya tsure da zawo; ko kuma […]

Jihohi sili da manuniyar sama

Batutuwa na bazuwa a kasar Haurobiya cewa jihohi sili da manuniyar sama babu tsaro a cikinsu, sai dai tsoro, kuma tushen wannan batu an ce ya fito ne daga kasar Uban-mama, wato Amari-kowa. Akwai al’amura kramin lauje, wato ko dai Amurkawa na son falla mana mari, su sanya kow aya tsure da zawo; ko kuma za su tabbatar da duban da suka yi cewa nan da shekara ta dubu karamin lauje da sili da  babban lauje kasa za ta tarwatse.
Ko ma dai mene ne nufin Amurkawa, mu mun san jiga-jigan Haurobiyawa ba sa aiki da hankali, ko kuma hankalinsu ya koma hannun riga. Domin duk sanda aka ankarar da kai cewa za ka iya fadawa rami idan ka cika zabari da gidingidimi a kan hanyar da kake gararamba, ai sai mutum ya sake salon tafiya. Ni dai ban yi mnazarin wannan labari a shafukan Dalilin-taronsu da Faffale-dalili da Balon-faranti da Gadin-yana da Banga-da-gadi, kai da daukacin mujallu da makalun da ake bugawa a kasar Haurobiyam, amma duk da haka zan iya yin has ashen wasu daga jihohin da ake yunkurin firgitawa. Mu dai yi aiki da hankali wanda ya fi aiki da agogo. Duk wanda ya yi wannan hasashe, matukar bai lalubo mana fagen gudun tsira ba, to yana da boyayyar manufa.
’Yan makaranta, masu koyon watsattsakee da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintattar jaridar kasar Haurobiya, ya zama dole ku fasko cewa, ana nufin al’ummomin da ke tsugunne a jihohin Yawon-Bebe da Alan-guburo da Bayan-Kada da dakin-kara da Tumbin-giwa da Ba-yasa da sauransu, su ake yi wa has ashen tsugunni-tsaye ba ta kare ba. Abin tuhuma ga Gwamnatin Haurobiya a nan, shi ne, idan abin da ke aukuwa a yabnkin Arewatawa ana danganta shi da Haramta Bobo da kwambon bobo, to a yankin Kadawa kuwa men ne dali? To ya kamata ku sani cewa rudani da rikita-rikitar jimurdar siyasa da ke aukuwa a yankin Kadawa, akwai hannun Shugaba Mai Gudun-loko da uwargida damo hakuri, da jami’an tsoratar da al’umma.
A Jihar Rababas, Uwargida Damo Hakuri, an sameta da hannu dumu-dumu wajen yamutsa jihar, don kawai ba ta ga maciji da Gwamna Mai aman-cici. Ga kuma dan Mai dan taku da kulki na Jihar, wato Mbu, wanda ke karya doka, maimakon tabbatar da ita.
Haurobiyawa, a hada karfi da karfe wajen kauce wa masu fafutikar tayar da yamutsi a kasar Haurobiya. Mu nemi maharba, wadanda za su harbor jirgin masu kai kawo don tabbatar da tsoro, suy haifar da rashin tsaro. Ina Damo-da-kura-da-diya. Kada mu zama, a lokacin da kura ke kokarin cinye mana diya.
A nan muna da zabi, ayyukan da ya kamata mu bai wa maharba, wato idan Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ce ke tada zaune-tsaye, saboda ta gaza warware badakalar Banga-Banga Tukuru, sai mu yi kokarin takureta. Idan kuwa Akuyar-maman-Daudu ce ke kokarin yada iskanci, tunda ita ’yar iska ce, kodayake wasu sun ce, ai ita ‘Jakadiyar sheke aya ce,’ to mu wancakalar da miyagun ayyukanta. Ko kuma Santala kwaiduwa ce ke son a manta da ta’asar da tafka? daukacin wadannan aika-aika da na jero duk ’ya’yan jam’ioyya mai dan boto da sanda jirge suka aikata su.
Duk da cewa Shugaba Jatau yana ikrarin yaki da kwashi kwaraf, kowa ya ji yadda ya nemi sau8ke Masanin Sisi-da-Sisi daga mukaminsa, alhali Santala kwaiduwa na nan na cin karenta babu babaka; uwa-uba ma, ta kera wa kanta shaidar karatun digirgire da digirin digirgir da sunan Jam’in jama’ar jami’o’in Amurkawa, amma har yanzu babu wani mataki da aka dauka a kanta.
danlele a Haurobiya shi ne gwanin tafka ta’asa. Yau Baba-ojo mai gonakin Ottawa ya rubutawa Banga-Banga Tukuru cewa ya daina tsallen badake a cikin harkokin jam’iyya.
Babban abin da nike son nusar da ku, shi ne, a tsofan Haurobiya na shekara dari sili, da kuma shekara babban lauje da kofar hanci da samun cin gashin kai, ba a taba mulkin keta haddin al’umma irin na Damo-da-kura-da-diya. Haurobiyawa, Mai danboto ita ce kura, ku kuwa al’umma kun zama damo, kun baje na-mujiya za a lakume muku diya (kasarku Haurobiya). Haurobiyawa kowa ya shiga taitayinsa, idan muna son tarayya, to mu tursasa Gwmana ta tarairayemu ba tare da nuna wariya ba; idan kuwa mun ga cewa dunkulewa zai yi mana wahala, to kamata yi ta ware ko ta yi warwaraye! Sai mu roki Mai-duka ya dora mu a kan turba, tun kafin Mai dan boto da sanda jirge ta jefa mu cikin rukwatubo.

Sakon makaranta
Assalam alaykum . Da fatan malam ya tashi cikin raha da karfin ‘body.’ Allah dai ya wadatamu da uwar jiki, amin.

Malam a balagorona na yawon buda wagagan shafuka a ragar mai gizo-gizo, duk da nasan cewa tuni ka fasko jirgin mai ‘Yar malfa ko ma dai in ce ka cika tumbinka fal da  manufofinsa. Gam da katar na yi da danyen hukuncin da ya rattaba wa hannu akai. ina ganin cewa ya kamata duk wani dalibi a makarantarka yayi  tur da al’amarin. Abban Ammar.

Kana nufin wariya da ake nunawa a tsakanin Haurobiya, ko kyale Santala kwaiduwa ta ci gaba da cin karenta babu babbaka? Ko ma dai me kake nufi, ya kamata ka fasko cewa miyagu na yunkurin jefa Haurobiya cikin ukwatubo