Jihohi uku a yankin Arewa maso Gabas za su zama tarihi – Mataimakin Gwamna

Ganin yadda mayaan Boko Haram ke samun galaba a jihohi uku na Borno da Adamawa da Yobe, idan gwamnati ba ta dauki kwakkwaran mataki a kai ba, jihohin za su koma karkashin mulkin Boko Haram kuma su zama tarihi. Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Zanna Umar Mustafa ya bayyana haka lokacin da yake magana da manema […]

Jihohi uku a yankin Arewa maso Gabas za su zama tarihi – Mataimakin Gwamna
Jihohi uku a yankin Arewa maso Gabas za su zama tarihi – Mataimakin Gwamna

Ganin yadda mayaan Boko Haram ke samun galaba a jihohi uku na Borno da Adamawa da Yobe, idan gwamnati ba ta dauki kwakkwaran mataki a kai ba, jihohin za su koma karkashin mulkin Boko Haram kuma su zama tarihi.

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Zanna Umar Mustafa ya bayyana haka lokacin da yake magana da manema labarai a Yola, inda ya ce idan Gwamnatin Tarayya ba ta dauki mataki a kan abin da ke faruwa a Arewa maso Gabas ba, akwai yiwuwar jihohin uku su zama tarihi.
Alhaji Zanna Mustafa ya ce “Idan gwamnati ta kasa daukar mataki a kan kungiyar Boko Haram, nan da wata uku jihohin uku za su zama tarihi.”
Ya ci gaba da cewa “Duk da cewa gwamnati tana kokari, ya kamata ta kara himma domin kokarinta bai wadatar ba. Saboda a kullum harkar ’yan bindigar gaba take yi.”
Mataimakin Gwamnan ya ce ya je Yola ne domin duba mutanen jiharsa da suka yi gudun hijira zuwa Yola sakamakon hare-haren da ’yan Boko Haram suka kai a kananan hukumomin Borno 13 da suka mamaye.
“kananan hukumomi 4 a Adamawa da 13 a Borno da wasu a Yobe duk suna karkashin ’yan bindiga Boko Haram bisa rahotun tsaro da muke da shi nan da ’yan makonni ’yan bindigar za su iya mamaye jihohin uku,” inji shi.
Mataimakin Gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta nemi agaji da taimakon kasashen waje domin yakar ’yan Boko Haram, tunda ta gaza yakar su.
Gwamnan Jihar Adamawa, Bala James Ngilari ya zub da hawaye kan halin da ya ga jama’arsa na shiga. Ya ce “Yanzu muna karkashin soja muna fatan za su yi aiki kwakkwara. In aka dage da addu’a komai zai yi sauki, mutane sama da miliyan 20 sun rasa rayukansu a Yakin Duniya na Biyu don haka ina da yakinin cewa wannan lamarin shi ma zai zo ya wuce.”

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi