Jihohin 13 za su fuskanci ambaliyar ruwa

Darakta Janar na Hukumar Yanayi ta Najeriya (NIHSA) Injiniya Clement Eze ya ce jihohin kasar 13 za su fuskanci aukuwar ambaliyar ruwa lura da yadda kogunan Binuwai da Neja ka kara cika. Injiniya Clement ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce jihohin su ne Neja da […]

Jihohin 13 za su fuskanci ambaliyar ruwa

Darakta Janar na Hukumar Yanayi ta Najeriya (NIHSA) Injiniya Clement Eze ya ce jihohin kasar 13 za su fuskanci aukuwar ambaliyar ruwa lura da yadda kogunan Binuwai da Neja ka kara cika.

Injiniya Clement ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce jihohin su ne Neja da Kwara da Kebbi da Nasarawa da Kogi da Edo da Delta da Ribas da Bayelsa da Taraba da Binuwai.

Ya ce kogunan Binuwai da Neja suna cika saboda yadda ake samun ruwan sama, sannan ya  ce ga ruwan da ke shigowa daga kasashe shida cikin kasashe 9 da suke kan Kogin Neja, inda ya ce dole abin ya kara ta’azzara.

Ya ce Najeriya ta kara shiga dar-dar ne bayan ambaliyar da ta auku a Jamhuriyyar Nijar wadda ake tsammanin za ta shigo ta Jihar Kebbi.

Ya ce bayanin da hukumarsu ta samu a ranar 6 ga Satumba daga Hukumar Kogunan Jamhuriyar Nijar ya nuna cewa ambaliyar Nijar ya kai nisan mita 6.26.

Sannan ya kara da cewa, Dam din Lagbo na kasar Kamaru ma yana kara cika, amma bai da masaniya ko za a sako shi ko ba za a sako shi ba a bana.

Ya ce hukumarsu tana bibbiyar ambaliyar da ke faruwa a kasar nan wadda ke jawo rasa rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sannan ya ce duk ambaliyar da ke faruwa a kasar dama can sun yi kashedin a kan faruwarta, inda ya ce mutane da masu ruwa-da-tsaki a bangaren da gwamnonin jihohi ne suke ki jin kashedin da suka bayarwa.

A wani labarin kuma, Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta shawarci mazauna yankunan da ake yi gargadin za su fuskanci ambaliya su dauki gargadin na Hukumar NIHSA da muhimmanci.

Darakta Janar na Hukumar NOA, Garba Abari ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, a shekaranjiya Laraba, inda ya ce jihohin da aka ambata da wadanda ba a ambata ba ya kamata su yi duk abin da ya kamata wajen kiyayen aukuwar lamarin.

Daga cikin abubuwan da ya kamata su yi kamar yadda ya lissafa akwai bude hanyoyin ruwa da hana zuba shara a hanyoyin ruwa da kiyaye tafiya a saman kwalbati a lokacin da ake ruwan sama da kuma kaurace wa bakin koguna.