Jihohin Arewa maso Yamma sun nemi a rage kudin mai da ake ba yankin Neja-Delta
Jihohin yankin Arewa maso Yamma sun nuna adawa da duk wani canji kan rabon arzikin kasa da zai kara wa jihohin yankin Neja-Delta kason kudin da ake samu daga albarkatun man fetur.Biyar daga cikin jihohin yanki da suka hada da Kano da Kebbi da Jigawa da Sakkwato da Zamfara sun ma nema a koma ga […]

Jihohin yankin Arewa maso Yamma sun nuna adawa da duk wani canji kan rabon arzikin kasa da zai kara wa jihohin yankin Neja-Delta kason kudin da ake samu daga albarkatun man fetur.
Biyar daga cikin jihohin yanki da suka hada da Kano da Kebbi da Jigawa da Sakkwato da Zamfara sun ma nema a koma ga tsohon tsarin rabon kashi 13 ciki 100 na kudin da aka samu daga man fetur ne da ke bambanta man da aka haka a teku da wanda aka haka a tudu.
Jihohin sun bayyana haka ne a lokacin sauraron ra’ayoyin jama’a kan rabon arzikin kasa na shiyya-shiyya da Hukumar Tattara Kudin Shiga da Rarraba su da kuma Tsara Albashi ta kasa (RMAFC) ta shirya a Kaduna a ranar Litinin da ta gabata.
Da yake gabatar da takarda a madadin Majalisar Dokokin Jihar Kano, shugabanta Gambo Sallau ya yi kiran a koma ga tsohon tsarin rabon kashi 13 na dukiyar maid a ake ba jihohin da suke samar da shi, ta yadda za a cire man da aka haka a cikin teku. Ya ce a shekara 14 ana aiwatar da sabon tsarin, tsarin ya haifar da “gibin da ba za a lamunce shi ba’ a tsakanin jihohin da suke samar da man fetur da mafi yawan kasar nan.
Shugaba Sallau, ya ce ba za su lamunci wani kari kan kashi 13 cikin 100 ba, maimakon sun zabi a koma ga tsohon tsarin bambanta man da ake haka a tudu da teku tare da soke dokar da ake amfani da ita a yanzu.
Ya ce “Mun hakkake an yi wa jihohin Neja-Delta abin da ya wajaba ta hanyar ba su kashi 13 da kafa Hukumar Raya Yankin Neja-Delta da Shirin Afuwa da kara kasafi ga yankin a karkashin wannan gwamnati da kuma kafa Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta.”
A yayin gabatar da nasu bukatun wakilan jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Jigawa sun ce bukatarsu ta zo daya da abin da Jihar Kano ta gabatar.
Shugaban Majalisar Jihar Kebbi Musa Habibu Jega da Babban Lauyan Jihar Zamfara Garba Mohammed da Babban Sakatare a Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar Jigawa Adamu Mu’azu da sauran wakilan sun ce sun goyi bayan shawarwarin da ’yan majalisar Kano suka gabatar.
Jihohin sun kuma nemi a yi gyara kan tsarin rabon arzikin kasa ta yadda za a rage kason Gwamnatin Tarayya a kara na jihohi. Kano ta bukaci kason Tarayya ya dawo kashi 41 da rabi daga kashi 52 da digo 68 cikin 100, a kara na jihohi zuwa kashi 34 da rabi maimakon kashi 26 da digo 72, sai na kananan hukumomi daga kashi 20 zuwa kashi 24 da rabi cikin 100.
Jihar Kebbi ta nemi a yi aiki da “Hakikanin dokar man da ake haka a tudu da teku ta shekarar 2004” inda ta ce iyakar teku an mika ta ga Najeriya ce a matsayinta na kasa bag a wata jiha a Najeriya domin haka babu iyakar teku a tsakanin wata jiha da wata jiha da ke kasar nan.
Ita kuma Jihar Sakkwato ta nemi tsarin rabon arzikin kasar ya kasance Gwamnatin Tarayya kashi 40 jihohi kashi 35 sai kananan hukumomi kashi 25 cikin 100.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya kawo shawarar a kirkiro Ma’aikatar Kula da Arewa domin magance matsalolinn rayyuwa da rashin tsaro ya haifar.
Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya fadi a jawabin bude taron cewa jihar “tana ba da cikakken goyon baya ga kara wa jihohi karfi, wanda zai hada da kara musu nauyin da karin albarkatu ga jihohi da kananan hukumomi.”