Zanga-zanga: Jihohin da suka sanya dokar hana fita

An haramta kowace irin zanga-zanga a fadin Jihar Katsina

Zanga-zanga: Jihohin da suka sanya dokar hana fita

Jihohin Kano, Jigawa, Yobe, Katsina da Borno sun sa dokar hana fita tsawon awa 24 sakamkon rikidewar zanga-zangar tsadar rayuwa zuwa tashin hankali da fasa shaguna ana sace kayan ciki.

Juigawa ranar Jigawa

Gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya sanar da kafar dokar a jihar ne a safiyar Juma’a, yana mai cewa ba zai lamunci yadda aka mayar da zanga-zangar lumanar a koma ashin hankali da sace sace ba. 

Sai dai ya ce za a sassauta dokar awa 24 din a fadin jihar daga karfe 12 zuwa 2.30 na rana domin Musulmi su samu damar yin Sallar Juma’a a masallatai.

Fadin Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar cewa, “Mun lura ya zama dole mu sa dokar hana fita tsawon awa 24 domin hana yadda ake kashe rayuka da fasa wuraren kasuwanci ana sace kayan ciki.”

Abba ya umarci jami’an tsaro su dauki mataki kan masu saba dokar, yana mai jinjina wa wadanda suka gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

Amma duk da haka, ya ce, “Abin  takaici ne yadda zanga-zangar da aka tsara a matsayin ta lumana ta koma hannun ’yan daba da ke sace-sace da ji wa jama’a rauni.”

Kananan hukumomi 3 a Yobe

A Jihar Yobe, an sa dokar hana fita ta tsawon awa 24 a kananan hukumomin Potiskum, Gashua da Nguru bayan bata-gari sun rika fasa wurare suna sace kayan ciki a lokacin zanga-zangar.

“Ana umartar jama’ar Potiskum, Gashua da Nguru su bi wannan doka su zauna a gidajensu domin samu zaman lafiya,” in ji sanarwar da mashawarcin gwamnan jihar kan al’amuran tsaro, Birgediya Dahiru Abdussallam (murasbu), ya sanya wa hannu.

Borno

Gwamnatin Borno a ta sanya dokar hana fita ta tsawon awa 24 sakamakon harin bom din kungiyar Boko Haram a kauyen Kauri da ke Karamar Hukumar Konduga, inda aka rasa rayuka 16 a jajibirin zanga-zangar.

Kwamshinan yada labarai da tsaron jihar, Farfesa Usman Tar, ya ce akwai matukar hadari a gudanar da zanga-zangar alhali gab da ita an kai harin bom din da ya yi sanadin kwantar da mutane 20 a asibiti, baya ga wadanda suka rasu.

A cewarsa, akwai yiwuwar ’yan ta’adda su shiga zanga-zangar su cutar da al’umma, shi ya sa aka sa dokar hana fitar.

Katsina

Mukaddadashin Gwamnan Katsina, Faruq Lawal, ya sanya dokar hana fita a fadin jihar.

Sanawar ta sa dokar hana fita ta sa’a 24 a Karmar Hukumar Dutsin-Ma, ragowar kananan hukumomi 33 na jihar kuma daga karfe 7 na dare zuwa 7 na safe.

Sanarwar ta kuma haramta kowace irin zanga-zanga a fadin jihar.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna