Jihohin da za a yi gumurzu a zaben bana
A wannan sabuwar shekarar da muka shiga ne za a gudanar da zaben gwamnoni a mafi yawan jihohin kasar nan, sai dai kuma ga dukkan alamu manyan jam’iyyun nan guda biyu watau PDP da APC sun tsayar da zakakarun ‘yan takara a jihohi da dama, wanda ya sanya za a yi artabu sosai wajen samun […]

A wannan sabuwar shekarar da muka shiga ne za a gudanar da zaben gwamnoni a mafi yawan jihohin kasar nan, sai dai kuma ga dukkan alamu manyan jam’iyyun nan guda biyu watau PDP da APC sun tsayar da zakakarun ‘yan takara a jihohi da dama, wanda ya sanya za a yi artabu sosai wajen samun wadanda za su zama gwamnoni a jihohin. Aminiya ta yi nazarin artatun da za a yi a wadansu jihohin kasar nan saboda karfin ‘yan takaran da aka tsayar kamar haka:
Daga Bashir Yahuza Malumfashi da Salihu Makera (Abuja), Kabiru Anwar (Adamawa), Misbahu Bashir (Kaduna), Habibu Umar Aminu (Katsina) Nurudeen Oyewole (Legas)
Adamawa:
A jihar Adamawa, akwai gumurzu mai girma, musamman ganin yadda kitimirmirar siyasa da kulle-kulle da asakala suka faru, musamman ma ganin yadda jam’iyyar PDP ta yi nasarar kwace kujerar daga hannun jam’iyyar APC.
Takarar kujerar gwamnan dai za ta kasance ne tsakanin Malam Nuhu Ribadu na PDP da kuma takwaransa na APC, Sanata Muhammad Jibrilla Bindow.
Masu nazarin harkokin siyasar jihar suna ganin cewa irin yadda uwar jam’iyyar PDP a Abuja take ba Malam Nuhu Ribadu goyon baya, musamman ganin yadda korafe-korafe suka biyo bayan zaben share fagen jam’iyyar, akwai yiwuwar wasu daga ’ya’yan jam’iyyar su ki mara masa baya, al’amarin da ake ganin zai taimaka wa dan takarar jam’iyyar APC ya samu galaba.
Haka kuma, wasu ’ya’yan jam’iyyar PDP a jihar sun canja sheka, suka koma jam’iyyar PDM, saboda nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zabubbukan share fage kwanakin baya. Irin wadannan mutane sun hada da Dokta Ahmad Modibbo da matarsa, A’ishatu dahiru Ahmad, wacce ’yar majalisar wakilai ce a Tarayya, mai wakiltar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei. A wannan karon, za ta yi takarar kujerar Sanata ne a jam’iyyar tasu. Haka shi ma Abdurrahman Kwaccam, wanda shi kuma zai fafata neman kujerar majalisar wakilai ta Tarayya a mazabar Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu da kuma Maiha.
Wadannan manyan ’yan siyasa da suka yi sabuwar sheka a PDM daga PDP, ana ganin za su jigata PDP, musamman ma ganin cewa suna da kumbar susa kuma suna da tasiri sosai a siyasance.
A yayin da Nuhu Ribadu na PDP da Modibbo na PDM ke shirin fara yakin neman zabe, shi kuwa Sanata Bindow, tun a watan Oktoban bara ne ya kaddamar da nasa yakin neman zaben, inda ya kewaya mazabu da dama kuma tarin magoya bayan da ya samu ya ba mutane mamaki. Ana ganin cewa idan ya jajirce kuma ya rike magoya bayan nasa, zai iya lashe zaben, ya zama Gwamnan Jihar Adamawa.
Wasu al’amura da za su taimaka masa, sun hada da ganin cewa jam’iyyarsu tana da karfi, ga shi kuma hamshakin dan siyasa, tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar yana goya masa baya. Haka ma farin jinin Janar Muhammad Buhari na iya tallafa masa ya kai ga nasara.
Ana hasashen cewa shi kansa Nuhu Ribadu na PDP ba kyallen yadawa ba ne, duk kuwa da cewa akwai rarrabuwar kai a jam’iyyar tasu. Duk kuma da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na jiha, Cif Joel Madaki da kuma yadda wasu ’yan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar suka rasa madafa. Irin sunan da Ribadu ya yi a lokacin da yake shugabancin hukumar EFCC, ana ganin cewa zai iya bunkasa ci gaban jihar idan ya zama gwamna. Ga shi kuma shaida ta tabbatar da cewa yana da goyon bayan fadar Shugaban kasa da kuma hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko dangote da kuma Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Adamu Mu’azu.
Kaduna:
A jihar Kaduna kuwa, takarar kujerar gwamna za ta kasance ne tsakanin giwaye biyu a jam’iyyun PDP da APC. Gwamna mai ci yanzu, Dokta Mukhtar Ramalan Yero na PDP ne zai kara da tsohon Ministan Abuja, Malam Nasiru el-Rufa’i na APC.
Jam’iyyar PDP dai ita ce ta kankane mulkin jihar tun daga 1999 da aka dawo da mulkin dimokuradiyya a Najeriya. Ita ke ta kafa gwamnati, kamar kuma yadda take samun rinjaye a majalisar jihar. Ganin cewa Gwamna Yero yana neman kujerar a karo na biyu ne, akwai yiwuwar ya yi nasara, tun da shi ke kan mulki. Haka kuma yana da goyon baya da tallafin Gwamnatin Tarayya, musamman ma ganin cewa Mataimakin Shugaban kasa dan jihar ne.
Wani abu da zai kawo wa PDP cikas a jihar shi ne, wasu da dama daga hamshakan jam’iyyar, wadanda kuma da su aka kafa ta, sun canza sheka suka koma APC. Abokin takarar Yero, Malam Nasiru zai iya cin gajiyar al’amarin, ganin yadda jam’iyyarsa ke da magoya baya da yawa a jihar. Ga shi kuma mutane na korafin cewa PDP ta kasa bunkasa jihar a tsawon lokacin da ta share tana mulki, wanda suke ganin cewa akwai bukatar su canza gwamnati a wannan karon.
Wani tagomashi da APC za ta samu a Kaduna shi ne, ganin cewa dan takarar shugabancin kasa, Janar Buhari na da dinbin magoya baya. Ta haka ne ake ganin za su iya kwarara wa el-Rufa’i ruwan kuri’u, ko don albarkacin Janar din.
Katsina:
A yayin da wasu jihohi ke da manyan ’yan takara biyu ko uku, ita Jihar Katsina tana da zaratan ’yan takara har guda biyar ne. Akwai Yakubu Lado na jam’iyyar PDM da Aminu Bello Masari na APC da Musa Nashuni na PDP da Abdulmumini Aliyu na NCP da kuma Umar Abdullahi Tsauri na APGA. Amma duk da yawansu, wadanda ake ganin sun fi tasiri su biyu ne, wato Masari na APC da kuma Nashuni na PDP.
Shi dai Nashuni bako ne a siyasa, za a iya cewa babu wanda ya san shi a siyasance, a jihar. Ya fara shiga al’amuran gwamnatin jihar ne a 2007, inda aka nada shi mukamin mai ba Gwamna Shema shawara ta fuskar Bunkasa Albarkatun kasa, daga bisani kuma aka nada shi Kwamishina a 2010.
Ana ganin cewa tun da Nashuni na da cikken goyon baya da hadin kan Gwamna Shema, akwai yiwuwar ya cin ma nasara, musamman ganin cewa gwamnan na yin amfani da dukkan abin da ke karkashin ikonsa wajen tallafa wa takararsa.
Idan muka dawo kan Masari kuwa, za mu gane cewa shi ba bakon siyasa ba ne, kasancewar a 2011 ya fafata neman kujerar ta gwamna tare da Shema a tsohuwar jam’iyyar CPC, duk da cewa bai samu nasara ba. Ganin cewa yana tare da Janar Buhari, wannan na iya ba shi damar samun kuri’u masu yawa. Haka kuma, akwai ’yan jam’iyyar PDP da yawa a jihar da ba su gamsu da zaben Nashuni ba, wanda haka na iya sanyawa su huce haushi, su ki zabensa.
Wani abu da zai taimaka wa Masari kuma shi ne, yadda ya fito daga bangaren Kudancin Katsina, bangaren da ke ganin cewa ya dace ya mulki jihar a wannan karon. Tun daga 1999 dai, Katsina ta tsakiya ce ke fitar da gwamna a jihar.
Yakubu Lado da Tsauri kuwa, ana ganin babu wani katabus da za su yi a zaben, ganin cewa ba su da magoya baya da yawa. Ana ganin cewa alamoninsu na jikin fosta-fosta ne kawai da kuma allunan kan hanya. Ana da yakinin cewa su kansu ba su da amannar samun nasara, sun dai shiga takarar ne kawai domin su kara bunkasa sunansu a siyasance.
Legas:
A Jihar Legas, ana ganin cewa fafatawar za ta kasance ne tsakanin giwaye biyu, Akin Ambode na APC da kuma Jimi Agbaje na PDP. Kuma ana ganin cewa iyayen gidansu ne abin lura a takarar.
Shi dai Ambode, zai ci gajiyar ubangidansa ne, wato Bola Tinubu. Ga shi kuma jam’iyyarsu ce ke mulkin jihar a halin yanzu. Haka kuma, kasancewar shi Ambode Kirista ne, hakan na iya kara masa martaba, mutane su zabe shi, musamman ganin cewa gwamnonin da suka mulki jihar a baya, Bola Tinubu da Fashola, dukkansu Musulmi ne.
Shi kuwa Agbaje na PDP, yana samun goyon baya ne daga Cif Bode George, wanda hamshakin dan siyasa ne a kasar Yarabawa. Haka kuma yana da goyon bayan tsohon Ministan Ayyuka, Adeseye Ogunlewe. Ana kyautata zaton, irin yadda wadannan mutane ke mara masa baya, akwai yiwuwar lallai ya kai ga gaci.
Wasu kuma na ganin cewa jam’iyyar PDP na iya kasa kai gaci a Legas, musamman idan aka yi la’akari da yadda zaben fitar da gwani ya gudana, inda kan ’yan takara da magoya baya suka rabu. Sai dai duk da haka, irin yadda Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo ya shiga tsakani, ya lallashi wadanda suke ganin an bata musu, hakan na iya dawo da martabar jam’iyyar.
Kamar yadda ta tabbata, Agbaje dai na da kakkarfan goyon bayan fadar Shugaban kasa, a wannan takara da yake yi, kuma hakan na iya yin tasiri wajen ganin ya samu nasara.
Sakkwato
A Jihar Sakkwato, manyan masu fafatawa a takarar Gwamnan surukan juna ne, wato Shugaban Majalisar Tarayya Aminu Waziri Tambuwal na Jam’iyyar APC da Sanata Abdullah Wali na PDP. Tambuwal yana auren daya daga cikin ’yan uwan Abdallah mai suna Mariya. Kuma dukkan ’yan takarar biyu sun fito ne daga karamar hukuma guda wato Tambuwal.
Kuma a yayin da Tambuwal ke takarar Gwamnan Sakkwato a karo na farko, Wali wanda Jakadan Najeriya ne a kasar Moroko, wannan ne karo na biyu da ya fito takarar don al’ummar Jihar Sakkwato su zabe shi a matsayin Gwamna.
Wani abin sha’awa Bafarawa da Wali a yanzu suna cikin Jam’iyya daya wato PDP, inda tsohon Gwamnan yake matukar goyon bayan Wali.
Shi kuwa Tambuwal da Gwamna mai ci Wamakko ne babban mai goya masa baya. Kuma Tambuwal yana takarar ce a karkashin jam’iyyar da ke mulkin jihar, yayin da Wali ke takara a karkashin gwamnatin da take mulki a matakin tarayya.
Kuma a yayin da Tambuwal da Wali suka sa zare don fafata zaben na 2015, masu sharhi suna ganin fafatawar za ta gudana ne don gwada kwanji a tsakanin tsohon Gwamna Bafarawa da Gwamna Wamakko mai ci wadanda manyan abokan gabar siyasa ne na dauri.
Nasarar wadannan ’yan takara za ta dogara ce kan fada a jin wadannan manya biyu da kuma karbuwar siyasar kowanne daga cikin ’yan takarar biyu don hayewa kan wannan kujera mai girma.
Nasarawa
A Jihar Nasarawa jam’iyyu biyar ne suka tsayar da ’yan takara a zaben na bana, inda APC ke neman a sake zaben Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, yayin da Yisuf Agabi ke rika wa PDP tuta don kalubalantarsa.
Sauran jam’iyyun uku su ne” LP da APGA da Accord Party da suka tsayar da Barista Lagi Innocent da Mathew Ombugaku da kuma Stanley Buba.
Al-Makura da babban abokin karawarsa, Agabi sun fito ne daga Lafiya da ke kudancin jihar, kuma dukkansu mutane ne da suka samu nasara a harkokinsu a baya.
Damar nasarar sake zaben Al-Makura a zaben bana tana tsaka-tsaki ne a tsakanin shi da Agabi wanda ya fito takara bisa goyon bayan manyan ’yan siyasar Nasarawa. Kuma a yayin da Al-Makura ke dogaro da rawar da ya taka a matsayinsa na Gwamna na farko da ya aza Jihar Nasarawa a bisa tubulin ci gaba, Agabi na da tagomashi a wurin jama’a, inda yake takama da soyayyar da suke nuna masa don samun kuri’unsu.
Al-Makura dai sun raba gari da shugabannin siyasa da suka goya masa baya ya shiga gidan gwamnati a shekarar 2011, don haka a yanzu zai dogara ne da talakawan jihar don ci gaba da zama a kan kujerarsa. Shi kuma Agabi yana zawarcin shugabannin siyasa ne da suka raba gari da Gwamnan.
Bauchi
Duk da cewa an samu takaddama wajen fitar da ’yan takarar manyan jam’iyyun nan biyu wato APC da PDP a Jihar Bauchi, akwai alamun za a fafata sosai a zaben na bana don ganin kowace jam’iyya ta kayar da abokiyar takararta.
Jam’iyyar PDP dai ta tsayar da dan Majalisar Tarayya Auwal Jatau a matsayin dan takarata, yayin da APC ta tsayar da wani fitaccen lauya Barista Muhammad Abubakar don rika mata tuta.
Fitar da ’yan takarar daga Bauchi ta Kudu da Bauchi ta Arewa da jam’iyyun biyu suka yi ya fusata mutanen yankin Bauchi ta Tsakiya musamman wadanda suka fito daga masarautar Misau, wadanda suka sa ran dansu Farfesa Ali Pate ya rika wa PDP tuta a wannan karo, lamarin da manzarta harkokin siyasar jihar ke ganin akwai yiwuwar a sake maimaita juyin juya-halin shekarar 2007, inda jama’a suka kawar da gwamnati mai ci ta PDP suka zabi ANPP.
Sai dai kuma ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare ganin kujerar Gwamnan jihar ta shafe shekara 16 a shiyyar Bauchi ta Kudu.