Jihohin Kano da Kaduna sun lashe gasar Alkur’ani ta kasa da aka yi a Legas
Jihohin Kano da Kaduna ne suka lashe gasar Alkur’ani na kasa karo na 34 wanda aka kammala a yau a Legas. A ranar juma’ar makon jiya, ranar 27 ga watan jiya Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar tare da gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu suka kaddamar da musabakar karatun Alkur’ani wadda ta sami halartar makarantu daga […]
Jihohin Kano da Kaduna ne suka lashe gasar Alkur’ani na kasa karo na 34 wanda aka kammala a yau a Legas.
A ranar juma’ar makon jiya, ranar 27 ga watan jiya Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar tare da gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu suka kaddamar da musabakar karatun Alkur’ani wadda ta sami halartar makarantu daga sassa daban daban na kasar nan.

Malam Umar Kabir, daga jihar Kaduna shi ne ya yi na daya a sashen maza yayin da Malama Diya’atu Sani Abdulkadir, tayi ta daya a sashen gasar na mata inda kowan nen su ya tashi da kyautar sabuwar mota kirar Nissan Almera, Jihar Legas mai masaukin baki ita ce tazo ta shida a gasar.