Jihohin Kano, Oyo da Osun sun ayyana hutun sabuwar shekarar Musulunci

Ranar Laraba ce dai daya ga watan farko na sabuwar shekarar

Jihohin Kano, Oyo da Osun sun ayyana hutun sabuwar shekarar Musulunci

Masallacin Kasa da ke Abuja

Jihohin Kano da Oyo da Osun sun ayyana Laraba, 19 ga watan Yulin 2023, a matsayin ranar hutu albarkacin sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.

Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana Larabar a matsayin ranar daya ga watan Almuharram na sabuwar shekarar, bayan hijirar Annabi Muhammad (S.A.W).

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye, ne ya fadi haka a cikin wata sanarwa a ranar Talata, a madadin Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.

Gwamna Abba ya taya Musulmai a fadin duniya murnar sabuwar shekarar, inda ya bukace su da su ci gaba da yi wa jihar addu’ar samun ci gaba da habakar tattalin arziki.

“Gwamnan ya kuma roki mutane da su yi amfani da kyawawan halayen addinin Musulunci na tausayi, kaunar juna da kuma kawaici, kamar yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar,” in ji sanarwar.

Shi ma Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaransa, Sulaimon Olanrewaju, ya fitar a Ibadan ranar Talata, ya ayyana ranar a matsayin hutu.

Gwamnan ya taya Musulmai murnar zagayowar sabuwar shekarar tare da bukatar su da su ci gaba da yin amfani da lokacin wajen yi wa Jihar da ma kasa baki daya addu’a.

Kazalika, Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, shi ma ayyana ranar a matsayin hutu, kamar yadda wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Addinai da Ayyuka na Musamman ta Jihar, Mudashiru Oyedeji, ya fitar ranar Talata.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara