Jihohin Neja-Dalta na bukatar rabin kason arzikin man fetur
A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne, Hukumar rabon arzikin kasar nan, wato RMAFC ta kammala sauraren ra`ayoyin Mahukuntan Jihohi da na kananan Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki akan tsarin rabon arzikin kasa, don sake fasalin rabon arzikin kasa, kamar yadda tanade-tanaden tsarin mulki suka tanadar mata ta rika yi daga […]
A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne, Hukumar rabon arzikin kasar nan, wato RMAFC ta kammala sauraren ra`ayoyin Mahukuntan Jihohi da na kananan Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki akan tsarin rabon arzikin kasa, don sake fasalin rabon arzikin kasa, kamar yadda tanade-tanaden tsarin mulki suka tanadar mata ta rika yi daga lokaci zuwa lokaci.
A yanzu dai kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, da aka yi wa kwaskwarima ya tanadi a raba arzikin kasar nan kamar haka;- Gwamnatin tarayya kashi 52.68, gwamnatocin jihohi ana ba su kashi 26.72, Majalisun kananan Hukumomi 774, kuwa suna da kashi 20 cikin 100. Kazalika a bangaren wani rabon arzikin kasar, akan kalli yawan jama`a da batun ilmi da samar da ruwan sha da kiwon lafiya da fadin kasa da irin kokarin da jiha ko karamar hukuma kan yi wajen tara kudaden shigarta da dai sauran batutuwa da kundin tsarin mulkin ya tanada.
Rabon arzikin kasar yakan kasance ne bayan an fitar wa jihohin nan bakwai masu arzikin man fetur kashi 13 cikin 100, na dukkan yawan kudaden arzikin man fetur din da aka tara, kafin ma rabon, man fetur din da ke samar da sama da kashi 90 cikin 100, na kudaden shiganr kasar nan. Tanade-tanaden tsarin mulkin shekarar 1999, suka bada damar a yi hakan ga jihohin tara, wadanda suka hada da jihar Akwa Ibom da Bayelsa da Ribas da Kuros Ribas da Edo da Delta da Imo da Ondo, sai jihar Anambra da ta shiga tsarin a `yan watannin nan. A zaman fafutika da gwagwarmar da ta kai ga daukar makamai da `yan yankin Neja Delta din suka rika yi a zaman hakar man fetur da ake yankunansu yana gurbata masu muhalli, don haka suka rika yin garkuwa da mutane da sauran ta`addanci iri-iri da ya kai matsayin ana samun koma baya akan man da ake hakowa, ta sanya a tsarin mulkin kasar nan da ake aiki da shi aka tanadi a rika ba gwamnatocin yanki kashi 13 cikin 100, na dukkan arzikin man da aka hako a yankunansu.
Duk da wannan tanadin kyautatawa da aka yi wa mutanen yankin Neja Delta din, manyan su da kananansu musamman tun daga watan Mayun 2010, lokacin da suka ga dansu Shugaba Dokta Goodluck Jonathan ke mulki, sai ya zama tamfar wani kaimi aka yi musu, ga dama ta samu sai barazana da arzikin man fetur nasu ne, don haka a ba su kayansu. Idan mai karatu bai manta ba ko a bara a daidai irin wannan lokaci da Majalisun Dokokin kasar nan suka gabatar da tarurrukan jin ra`ayoyin jama`a akan gyaran kundin tsarin mulki, sai da wannan batu ya taso, inda suka nemi a ba su abinsu gaba daya.
A wannan karon ma da Hukumar ta RMAFC, ta dukufa, wajen gyaran tsarin yadda rabon arzikin zai kasance, a zamanta na jin ra`ayoyin jama`a, wanda ta yi a Yenagoa babban birnin Jihar Bayelsa, inda jihohin Kudu maso kudu suka gabatar da bukatarsu, an ruwaito Sakataren gwamnatin jihar ta Bayelsa, Farfesa Edmund Allison Oguru da ya wakilci gwamnan jihar Cif Siake Henry Dickson, bayan ya shawarci Hukumar ta RMAFC da lallai ta mayar da kaso 13, cikin 100, da yanzu ake ba jihohinsu zuwa 50, cikin 100, bayan ta rage kason da ake ba gwamnatin tarayya, wanda a fadarsu yawan kudin da ake ba gwamnatin tarayyar, ke sa wasu mayar da neman shugabancin kasar nan wani abin “a mutu ko a yi rai”.
An ruwaito Gwamnan Jihar Bayelsa yana fadi a wajen taron cewar lallai sai Hukumar ta RMAFC, ta rage kason da take raba arzikin kasar akan yawan jama`a daga kashi 40,zuwa kashi 10, cikin 100, don a fadarsa, babu wasu tartiban alkalumma akan sahihancin kidayar kasar nan.
Dukkan sauran shiyoyin kasar nan da suka gabatar da ra`ayoyinsu a zaman shiyyoyinsu da aka yi, sun yi kira ga Hukumar ta RMAFC, da lallai ta rage rabon da ake ba gwamnatin tarayya da aniyar ta kara shi ga jihohi da kananan hukumomi, ta kuma bar kashi 13 cikin 100, da ake ba jihohi masu arzikin man fetur, kamar yadda yake yanzu. Alal misali a zaman shiyyar Arewa maso yamma da aka yi Kaduna an ruwaito Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Alhaji Gambo Sallau ya nemi da a koma tsarin rabon arziki kasa irin na da kafin shigowar wannan jamhuriyar. Wannan sabon tsarin kamar yadda ya ce yana haifar da matsalolin rayuwa da banbance-bambance tsakanin mutanen kasar nan, abin da ya ce gwamnatin jiharsa ba ta goyon bayansa, bare har a yi karin ko sisin kwabo akansa. Ya kuma waiwayi sauran sassa irinsu ilmi da yawan jama`a da akan yi amfani da su wajen rabon arzikin da a duba su da idon rahama da aniyar yin kari ko ragi inda ya kamata, bayan ya nemi a rage kason gwamnatin tarayya don kari ga sauran hukumomi.
Wannan matsayi na Jihar Kano, shi Jami`an gwamnatocin jihohin Kabbi da Jigawa da Zamfara, suka amince da shi. Ya yin da a zaman shiyyar Arewa maso Yamma da aka yi a Bauchi, mahukuntar shiyyar suka nemi gwamnatin tarayya da ta kafa masu Hukumar da za ta fara aikin nemo mai a shiyyar, tunda kuwa akwai shi.
Mai karatu ka iya cewa kowa ya samu rana sai ya yi shanya, amma wannan shanyar in har aka bar masu yinta suka ci gaba , to, kayayyakinsu za su yi ta bushewa har suna guga, na sauran abokan zama kuma suna ruwa, ba su ma wanku ba bare a shanya su bushe. A yadda ake yanzu ba shiyyar da take ’yargata irin shiyyar ta Neja Delta. Baya ga wadancan kaso 13, da aka kebe masu, sannan an yi masu Ma`aikatar kula da yankinsu,sai kuma Hukumar raya yankin da ake da ita, wato NDDC sai kuma tayin afuwa da marigayi tsohon shugaban kasa, Alhaji Umaru `Yar`aduwa ya yi wa tsagerunsu da yanzu ake tura su karatu a kasashen duniya daban-daban, ga makudan kudi da gwamnatin tarayya take kashe wa yankin a cikin kasafin kudin kasa na duk shekara, ko a kasafin kudin bana an ce an fi kashe wa shiyyar kaso mafi tsoka.
In sun samu kashi 50, cikin 100, ko mu ce rabi na arzikin man fetur din kasar nan sauran `yan kasa kuma su shiga ina? kalubale ga wakilanmu na Majalisun Dokokin jihohi da na tarayya da kuma wadanda za su Wakilce mu a taron tattauna matsalolin kasa.
Ina yi wa dukkan masu karatu musulmi Barka Da Sallah da addu`ar Allah Ya dawo da alhazanmu lafiya.