Jikan Mandela ‘ya Musulunta’

Wani Malami wanda ya daura auren jikan tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, mai suna Mandla, ya ce dan shekara 42 din ya karbi addinin Musulunci a bara, kamar yadda rahotanni wasu jaridun kasar suka bayyana a ranar Litinin.“Zan iya cewa abin alfahari ne da na daura auren jikan shugabanmu, Nelson Mandela,” in […]

Jikan Mandela ‘ya Musulunta’
Jikan Mandela ‘ya Musulunta’

Wani Malami wanda ya daura auren jikan tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, mai suna Mandla, ya ce dan shekara 42 din ya karbi addinin Musulunci a bara, kamar yadda rahotanni wasu jaridun kasar suka bayyana a ranar Litinin.
“Zan iya cewa abin alfahari ne da na daura auren jikan shugabanmu, Nelson Mandela,” in ji Sheikh Ebrahim Gabriel, wanda ya daura auren a wani Masallaci a birnin Cape Town a ranar Asabar.
Jaridar mai suna IOL ta ce malamin ya ce ba zai bayyana adadin sadakin da jikan Mandela ya biya ba tukuna, saboda magana ce “ta sirri tsakanin mata da miji”.
Mandla wanda dan majalisar dokoki ne kuma basaraken gargajiya, bai mayar da martani ba a kan addinin da yake bi.
Kodayake, wannan ne aurensa na hudu, kuma sunan sabuwar amaryarta sa Rabi’a Clarke. A shekaranjiya Laraba Majalisar Sarakunan  kasar ta bayyana rashin gamsuwarta game da yadda Mandlan ya karbi addinin Musulunci.