Jikar Buhari ta haifa masa tattaba-kunne na farko

Mai jegon ’ya ce ga babbar ’yar Buhari ta biyu, Fatima. 

Jikar Buhari ta haifa masa tattaba-kunne na farko

Aisha Mukhtar, jika ga Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari, ta haifa masa tattaba-kunnensa na farko.

Mai jegon, wadda ta auri Khalid Wambai a 2021, ’ya ce ga babbar ’yar Buhari ta biyu, Fatima.

Aisha Mukhar mamba ce a Cibiyar Kwararrun Masu Binciken Zamani Kan Zamba ta Najeriya (CIFCFEN).

Yanzu haka dai Buharin na da ’ya ’ya 10, amma biyu sun rasu, biyar daga ciki kuma ya haife su ne tare da tsohuwar matsrsa, Safinatu Yusuf wacce suka rabu a shekarar 1988.

Daga baya ya auri Aisha wacce ita ce matarsa har zuwa yanzu.