Jikar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela ta rasu

Zoleka, jikar jagoran gwagwarmayar samun ’yancin kasar Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, ta rasu tana da shekaru 43.

Jikar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela ta rasu

Zoleka, jikar jagoran gwagwarmayar samun ’yancin kasar Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, ta rasu tana da shekaru 43.

A safiyar Talata ne iyalan Mandela suka sanar da rasuwar Zoleka bayan fama da cutar kansa.

Kakakin iyalan, Zwelabo Mandela, ya ce a ranar Litinin ta je asibiti domin ganin likita, inda daga bisani “rai ya yi halinsa a gaban ’yan uwa da abokan arziki.”

Ya ce a baya-baya nan, cutar “ta yi mata illa a kwakwalwarta da lakarta, da kuma hanta da huhu da kuma kashin baya.”

Marigayiya Zoleka, ’ya ce ga ’yar autar Mandela, Zindzi da mijinta na farko Zwelibanzi Hlongwane.

Gidauniyar Nelson Mandela ta rubuta a shafinta na sada zumunta cewa, “Muna juyayin rasuwar jikarmu (Zoleka) ’ya ga Winnie da kuma Madiba (Mandela).”Aikin da ta yi na wayar da kan al’umma kan cutar kansa da kuma hana tsangwamar masu cutar abubuwa ne da ba za a taba mantawa ba.