Jikin Ashiru Nagoma da sauki —Fauziyya D. Suleiman

Fitacciyar marubuci, kuma shugabar gidauniyar Creative Helping Needy Foundation, Hajiya Fauziyya D. Suleiman ta tabbatar da rashin lafiyar Ashiru Nagoma. Marubuciyar ta bayyana wa Aminiya cewa jikin daraktan na masana’antar fim ta Kannywood, da sauki inda ake kula da shi a asibiti. Kannywood ta zama kasuwar bukata –  Zango An kai daraktan Kannywood Ashiru Nagoma […]

Jikin Ashiru Nagoma da sauki —Fauziyya D. Suleiman

Hajiya Fauziyya tare da wasu daga cikin wadanda suka kai darakta Ashiru Nagoma asibiti

Fitacciyar marubuci, kuma shugabar gidauniyar Creative Helping Needy Foundation, Hajiya Fauziyya D. Suleiman ta tabbatar da rashin lafiyar Ashiru Nagoma.

Marubuciyar ta bayyana wa Aminiya cewa jikin daraktan na masana’antar fim ta Kannywood, da sauki inda ake kula da shi a asibiti.

A cewar Fauziyya, “jikin da sauki. Idan kana magana da shi, zai ka ga kamar yana da hankali, sai dai daga baya ya dan saki layi.”

Aminiya ta zanta da Fauziyya ne bayan gidauniyarta ta kai daraktan asibiti, bayan rahotannin da ke cewa yana fama da lalurar tabin hankali.

Fitacciyar marubuciyar, wadda ta yi fice wajen daukar nauyin marasa lafiya a ciki da wajen Najeriya ta kara da cewa, “akwai alamar damuwa, akwai rashin kula.

“Ka san ba shi da mata, kuma ya rasa iyayensa, sannan kuma harkar ta ja baya da shi.

“Amma idan kuna magana, yana fahimtar komai, sai dai daga baya ya[kan yi] kwaba; sai kuma rashin askin nan da ba ya yi. Amma da sauki.”

Da Aminiya ta tambaye ta ko jaruman Kannywood suna wani abu, sai ta ce dama sun yi kokarin haka, amma sun ce ’yan uwansa suka hana, sai dai ’yan uwan nasa suka ce ba haka ba ne.

“Amma dai yanzu gidauniyarmu dama sun mun ce za mu dauki nauyin maganinsa.

“Sannan wasu jaruman da muka yi magana da su sun nuna a shirye suke su taimaka.”

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54