Jima’i: Guzurin bayanai ga matan aure (3)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. Kamar yadda wadansunku suka sani ne jikin namiji yana da wadansu wurare ko gabobi da suke motsa masa sha’awa, amma da yawan wadansu mata ba su fahimci wuraren ba, to namiji yana da wurare 9 da suke motsa masa sha’awa, […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. Kamar yadda wadansunku suka sani ne jikin namiji yana da wadansu wurare ko gabobi da suke motsa masa sha’awa, amma da yawan wadansu mata ba su fahimci wuraren ba, to namiji yana da wurare 9 da suke motsa masa sha’awa, sannan su ba shi gamsuwa a wajen bangaren jima’i.
A wannan makon guzurin da na yi muku shi ne, zan yi muku bayanin wadannan wurare tara don su kasance wani sirri a wurinku da za ku rika sarrafa mazajensu yayin jima’i cikin ruwan sanyi.
Wadannan wurare suna dauke da jijiyoyi wadanda kai tsaye suke aika sako zuwa kwakwalwa cikin kankanen lokaci. Wadannan wurare sun hada da:
1. Cikin leben kasan baki
Bakin namiji wuri ne da ke saurin aika sako zuwa kwakwalwa, kuma ga namiji yana saurin motsa masa sha’awa. Ba wai na sanar da ku wannan wurin sai kuma ku rika nacewa wajen tsotsar leben mijinku ba, hakan zai sanya ya ji kun gundure shi, lokaci zuwa lokaci za ku rika tsotsar wajen kasan lebe.
A jikin lebe akwai wadansu kananan jijiyoyi wadanda suke motsa sha’awa cikin kankanen lokaci.
Yadda za ku yi: A lokacin da kuke son motso da sha’awar mijinku, sai ku tura leben kasan bakin mijinku cikin bakinku, sannan ku rika amfani da tsinin harshenku kuna wasa da shi a kan fatar leben mai dauke da tarin kananan jijiyoyi masu isar da sako ga kwakwalwa. Za ku ci gaba da zuwa da dawowa da harshenku, inda hakan zai sanya mijinku ya tafi wata duniya cikin jin dadi. Zai rika jin kamar ana yi masa susa mai dadi a bakinsa ne.
Wani abu da nake so in ja hankalinku shi ne, ku rika kula da bakinku, ma’ana ku tsaftace shi ta hanyar goge bakinku sau biyu ko uku a rana, ko kuma daf da lokacin da kuke so ku sumbaci mijinku don kada ya rika jin kyamarku, idan har kuna so tsotsar lebe ya kara armashi, to za ku iya sanya minti mai zaki a bakinku, walau lokacin da kuke tsotson ko kuma kafin, hakan zai sanya yawun bakinku ya kasance cikin zaki da kuma kamshin mintin.
2. Gaban Wuya
Yawancin mata ba su da masaniyar cewa wuya na motsa sha’awar namiji, wadanda suka sani kuma sun fi mayar da hankali wajen shafa gefen wuya ne, amma a zahirin gaskiya wurin da ya fi motsa wa namiji sha’awa a wuya shi ne gaban wayansa daidai saitin makogwaro, domin akwai kororon da ya wuce har zuwa cikin ciki, kuma wannan kororon yana dauke da jijiyoyin kanana da kai tsaye suke tura sako ga kwakwalwa, sannan suna taka muhimmiyar rawa wajen motsa sha’awar namiji. Wani masanin magani dan kasar China mai suna Mantak Chia, ya bayyana makogwaro yana dauke da jijiyoyin da suke da kusanci da gabobin sha’awa.
Yadda za ku yi: Ku kwantar da mijinku a kan filo kamar yadda kuke kwantar da jariri, wato ya kwanta da bayansa kansa ya kalli sama, hakan zai ba ku damar ganin ko’ina a wuyansa. Daga nan ku yi amfani da harshenku wajen lashe wuyansa, musamman ma kan makogwaronsa, daga nan ku ci gaba da wasa da harshenku a wuyansa har zuwa daidai habarsa. Za ku iya amfani da hannunku wajen yi wa wuyan tausa, musamman ga namijin da yake da bayyanannun jijiyoyi a wuyansa ko kuma makogwaron wuya.
3. Cibiya
Cibiya wani wuri ne na matattarar sha’awar dan Adam, amma mata ba su cika mayar da hankali wajen amfani da ita wajen sosa ran mijinsu ba.
Yadda za ku yi: A wannan lokacin ma za ku kwantar da mijinku a kan matashin kai, kansa ya kalli sama, sannan ku yi amfani da yatsunku wajen sosa masa cibiya, ko ku rika zagaya shatin cibiyar da yatsunku. Wani salo da za ku yi amfani da shi ne, amfani da harshenku wajen lashe cibiyar, sannan idan mijinku yana da kwarin cibiya, za ku iya zuba yawunku a cikin sannan ku rika kada harshenku a ciki, za ku ga yadda zai rika numfarfashi da gurnani. Idan kun jika cibiyarsa da yawunku, za ku rika hurawa, iskar da za ta sauka a cibiyar za ta sa sha’awar mijinku ta motsa. Sannan za ku iya tsotsar cibiyar ko sosa ta da hakoranku. Za ku kuma iya cizonta amma ba da karfi ba.
Wata hanya da za ku bi wajen kara rikitar da mijinku shi ne, za ku iya shan kankarar ice cream, ko ruwa mai sanyi, hakan zai sanya harshenku ya dauki sanyi, idan kuka dora harshenku a kan cibiyar mijinku zai ji kamar ana bibration a cibiyarsa, har bai san lokacin da zai rungume ki a jikinsa ba.
Za mu ci gaba.
Domin karin bayani za ku iya tuntubar Bashir Liman a wannan lambar 07036925654.